Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-08 18:43:33    
Ana bunkasa tattalin arzikin lardin Shandong na kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba

cri

Ka zalika gwamnatin lardin Shandong ma ta dauki matakai masu yawa wajen ba da taimako don bunkasa harkokin tattalin arziki ba tare da gurbacewar muhalli ba. Tun daga shekarar 2005, gwamnatin ta ware makudan kudade musamman domin gudanar da harkokin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbacewar muhalli. Malam Guo Shuyu, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin cinikin waje ta lardin Shandong ya bayyana cewa, nan gaba lardin zai kara kokari wajen yin amfani da albarkatun kasa sosai. Ya kara da cewa, "lardin Shandong zai yi kokari sosai wajen yin amfani da albarkatun kasa daga fannoni daban daban da kuma yin amfani da datti da juji. Zai nuna himma ga yadada hanyar zamani da ake bi wajen amfani da albarkatun kasa daga duk fannoni, kuma zai kokarta wajen yin amfani da datti da juji musamman dagwalo da hayaki da kazantaccen ruwa."

Bisa kokarin da aka yi ta yi a cikin 'yan shekaru da suka wuce, yawan makamashi da aka yi amfani da shi don samar da kayayyaki a duk lardin a shekarar 2006 ya ragu da kashi 3.4 cikin dari bisa na shekarar 2005. Sa'an nan yawan muhimman abubuwa masu gurbata muhalli da aka fitar a duk lardin ma ya ragu da kashi 2 cikin dari. Ta haka lardin Shandong ya kyautata muhallinsa a bayyane ta hanyar tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurtacewar muhalli da ake fitarwa. (Halilu)


1 2