Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-08 18:43:33    
Ana bunkasa tattalin arzikin lardin Shandong na kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba

cri

Lardin Shandong da ke a gabashin kasar Sin wani babban lardin kasar ne a fannin tattalin arziki da yawan mutane. A cikin wani tsawon lokaci da ya wuce, da yake aikin masana'antu yana da muhimmanci sosai ga tsarin tattalin arzikinsa, lardin Shandong ya zama daya daga cikin manyan larduna da ke amfani da albarkatu masu dimbin yawa a kasar Sin. Amma a cikin shekarun nan da suka wuce, lardin ya bunkasa harkokin tattalin arzikinsa ne ba tare da gurbacewar muhalli ba, ta sabuwar hanyar da take bi wajen tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli da yake fitarwa, kuma ya sami kyakkyawan sakamako a fannonin zamantakewar al'umma da na tattalin arziki.

Babban kamfanin narke karafa na birnin Jinan , fadar gwamantin lardin Shandong wanda ya kafu a shekarar 1958, yana daya daga cikin kamfanoni mafi girma a lardin. Nauyin bakin karfe da yake fitarwa ya wuce Tan miliyan 10 a ko wace shekara. A da, kazantaccen ruwa da hayaki da kamfanin ya fitar sun gurbata muhallin duk birnin, amma yanzu ba haka ba ne. Malam Xu Tao, shugaban hukumar kula da harkokin makamashi na kamfanin ya bayyana cewa, "a da, kamfaninmu ba ya amfani da hayaki da yake fitarwa, don haka ba ma kawai an bata makamashi ba, har ma an gurbata muhalli. Amma yanzu muna aiki da injunan wuta da ke amfani da hayakin da kamfaninmu ke fitarwa wajen samar da wutar lantarki, ta haka mun riga mun sami kyakkyawan sakamako a fannin tattalin arziki da na muhalli. "

An ruwaito cewa, yawan wutar lantarki da kamfanin nan ke samarwa da kansa ya kai kusan kilowatts awa miliyan 8 a ko wace rana, wato ke nan ya dauki kashi 60 cikin dari bisa jimlar wutar lantarki da kamfanin ke bukata a ko wace rana.

Kamfanin kera manyan motoci masu daukar kaya na kasar Sin da ke a birnin Jinan, fadar gwamnatin lardin Shandong wani babban sansanin kera manyan motoci masu daukar kaya ne a kasar Sin. Wani reshen da kamfanin ya kafa a shekarar 1998, yana yin kwaskwarima a kan tsoffin injunan manyan motoci masu daukar kaya tamkar sabbabi. Farashin irin wadannan injuna kuma ya dauki rabin kudi bisa na sabbabi kawai. Da malam Cai Dong, babban majanan reshen kamfanin ya tabo magana a kan aikin reshensa, sai ya ce, "yanzu, reshenmu ya kafa wuraren ba da hidima sama da 600 da kuma wuraren saye da sayar da injunan motoci sama da 600 a kasar Sin. Muna sayen tsofaffin injuna a wuraren. Wato idan wani injin motar na bukatar kwaskwarima sosai, to, za mu canja shi da wani injin da muka riga muka yi masa kwaskwarima, kudin da ake biya kuma kadan ne. Irin wannan inji da muka hada shi da mota ya tashi daidai da sabo, t haka dai ne yawan irin injunan da muka sayar ya karu cikin sauri."

1 2