Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-28 20:20:22    
Gidan rediyon kasar Sin na kokarin bunkasa sabbin kafofin yada labarai

cri

Gidan rediyon kasar Sin wanda ke da tsawon tarihi na shekaru 65, a yanzu haka, yana watsa labarai cikin harsuna 43 a kowace rana ga kasashe da shiyyoyin da yawansu ya zarce 200. A yayin da yake cigaba da inganta hanyoyinta na gargajiya na watsa labarai, wato rediyo, a cikin 'yan shekarun nan, gidan rediyon kasar Sin ya kuma fara kokarin bunkasa sabbin kafofin yada labarai. Tasharmu ta internet, wato CRI Online, wanda aka bude a shekarar 1998, ya kasance wani mafari na wannan babban aikin da gidan rediyon kasar Sin ke yi na bunkasa sabbin kafofin yada labarai, kuma gidan rediyon kasar Sin ya sami cigaba cikin sauri a kokarinta na bunkasa sabbin kafofin yada labarai. Ya zuwa karshen shekarar 2002, gidan rediyon kasar Sin ya riga ya bude shafunan internet da ke amfani da dukan harsunan waje 38 da yake da su. Sa'an nan, a shekarar 2005, gidan rediyon kasar Sin ya kuma gabatar da shirye-shiryensa na rediyon da aka iya saurara ta hanyar internet. A shekarar 2006, ya gabatar da Podcasts, wato shafunan internet da masu sauraronsa suke iya manne bayanai na audio da video da na karatu a ciki. Sai kuma a watan Maris na shekarar da muke ciki, gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da shirye-shiryen Telebijin da aka iya kallo ta hanyar internet. Daga baya, a watan Afrilu, ya kuma gabatar da shirye-shiryen rediyo da telebijin da aka iya kama su ta hanyar wayar salula.

Sakamakon yin amfani da sabuwar fasaha, yanzu gidan rediyon kasar Sin na kara bayar da tasirinsa fiye da yadda yake dogara ga rediyo kawai a da. Bisa cigaban kimiyya da fasaha, a nan gaba, gidan rediyon kasar Sin zai ci gaba da bunkasa sabbin kafofin yada labarai. (Lubabatu)


1 2