Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-28 20:20:22    
Gidan rediyon kasar Sin na kokarin bunkasa sabbin kafofin yada labarai

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Badamasi Mohammed Palladan, mazaunin garin Zaria da ke tarayyar Nijeriya. Kwanan nan, bayan da malam Badamasi Mohammed ya karanta wani bayani a shafinmu na internet, dangane da kokarin kafa sabbin kafofin yada labarai da gidan rediyon kasar Sin ke yi, sai ya rubuto mana cewa, shin ko za ku yi mana bayanin hanyoyin watsa labarai na gargajiya? Don ban gane ba, ina bukatar bayani daga gare ku. To, bari mu yi muku takaitaccen bayani a kan irin sabbin kafofin yada labarai da gidan rediyon kasar Sin ke kokarin kafawa, gwargwadon hanyoyin watsa labarai na gargajiya.

Hanyoyin watsa labarai na gargajiya na nufin rediyo da telebijin da jaridu, wadanda aka dade ana amfani da su wajen watsa labarai. Amma bisa cigaban kimiyya da fasahohi, wasu sabbin fasahohi na zamani sun bullo, wadanda suka hada da fasahar internet da fasahar digital da dai sauransu, har ma an fara amfani da su a wajen watsa labarai, sabo da haka kuma, sabbin kafofin yada labarai sun fito, ciki har da internet da IPTV da gidan rediyo da gidan telebijin da aka yi ta wayar salula. Bisa karin cigaban kimiyya da fasaha, za a kuma fito da sauran sabbin kafofin yada labarai.

Watakila akwai masu sauraron da ke tambaya, me ya sa gidan rediyon Sin ke kokarin bunkasa sabbin kafofi na yada labarai? Amsa shi ne, bisa cigaban kimiyya, ya zama dole a kama sabbin fasahohi, idan ba a so ba bar shi baya ba.

1 2