Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-28 17:51:39    
Ra'ayoyin mutanen kasashen ketare kan babban taron wakilan kasa na 17 na JKS

cri

Jam'iyyar Kwaminis ta Sin jam'iyya ce da ke rike da mulkin kasar. Abhisit Vejjajiva, shugaban jam'iyyar dimokuradiyya ta kasar Thailand ya bayyana ra'ayinsa a kan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin cewa, "Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta dade tana kula da harkokin kasar Sin. A ganina, daya daga cikin kyawawan sakamakon da ta samu shi ne, ta iya kyautata hanyar da kasar Sin ke bi don samun bunkasuwa bisa sauyin al'amuran duniya. A cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta sami babban ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinta, wannan ya jawo hankulan mutanen duk duniya kuma ya sami amincewa daga wajensu. Amma kula da wata babbar gamayyar tattalin arziki bisa sauye-sauyen al'amuran duniya ba wani abu mai sauki ba ne. Sabo da haka ina ganin cewa, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta kware sosai wajen kyautata hanyar da kasar ke bi wajen samun bunkasuwa bisa sauyin halin da ake ciki. Jam'iyyar nan wata jam'iyyar siyasa ce mai hangen nesa." (Halilu)


1 2