Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-28 17:51:39    
Ra'ayoyin mutanen kasashen ketare kan babban taron wakilan kasa na 17 na JKS

cri

Za a fara yin babban taron wakilan kasa na karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a nan birnin Beijing a ran 15 ga watan gobe. A galibi dai, ra'ayoyin jama'a na ganin cewa, taron zai kawo tasiri mai muhimmanci ga ci gaban harkokin siyasa da na tattalin arzikin kasar Sin. A kwanakin nan, wakilan gidan rediyonmu da ke zama a kasashen waje sun kai ziyara ga 'yan siyasa da masanan ilmi na kasashe da dama don jin ta bakinsu a kan wannan taro da abubuwan da taron ya shafa.

Da Fazal-ur-Rahman, shugaban sashen nazarin kasar Sin na cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Pakistan ya tabo magana a kan babban taron wakilan kasa na karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da za a kira nan gaba ba da dadewa ba, sai ya ce, "a ganina, gaskiya ne, kiran babban taron nan wani al'amari ne mai muhimmanci. An kuma shirya taron ne, yayin da muke ganin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni da yawa, ana cikin wani lokacin da ya kamata a yi bayani a kan aikin kwaskwari da na bunkasuwar da ake yi a kasar Sin, yanzu kuma ana cikin wani lokaci mai muhimmanci ga raya kasar Sin. Babban taron wakilan nan zai gabatar da ka'idojin da za a bi wajen tsara shirin raya kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa."

Ogaba Oche, masanin ilmin batutuwan kasar Sin na cibiyar nazarin batutuwan duniya ta kasar Nijeriya ya bayyana ra'ayinsa a kan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin cewa, "yayin da muka tabo magana a kan kasar Sin, sai mu yi magana a kan irin wannan kasa mai dogon tarihi da mutane da yawa, amma Jam'iyyar Kwaminis ta Sin tana sauke nauyinta yadda ya kamata na jagorancin wannan kasa, tana shugabancin kasar Sin ga raya kasar Sin ta zamani cikin sauri sosai. Idan an so a kula da irin wannan bunkasuwa da ake samu da fuskantar tasirin da ake haifar a fannoni da yawa, to, wannan zai zama babban kalubale ne ga wata jam'iyyar siyasa. Duk da haka Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta yi aikinta da kyau, kuma ta sami babbar nasara."

Haka kuma da shehun malami Gustaaf Geeraerts, shugaban kolejin koyon ilmin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da siyasa na Jami'ar Liberalism ta birnin Brussels na kasar Belgium ya bayyana ra'ayinsa a kan babban taron wakilan kasa na karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, sai ya bayyana cewa, "a ganina, babban taron nan yana da muhimmanci sosai. Dalilin da ya sa haka shi ne ta hanyar babban taron, za a kara fahimtar hanyar da kasar Sin ke bi cikin sauki wajen samun bunkasa a nan gaba. Babban sakatare Hu Jintao zai gabatar da shirye-shiryensa na daidaita matsalolin da kasar Sin ke fuskanta na rashin daidaicin zamantakewar jama'a da yanayin kasa da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a da sauransu. Wadannan matsaloli manyan matsaloli ne da kasar Sin ke fuskanta a fannin zamantakewar al'umma."

1 2