Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-27 14:15:10    
Taro na 17 na wakilan duk kasa na JKS wani taro ne na al'ada da bude wata sabuwar makoma cikin yunkurin bunkasa kasar

cri
 

A ran 7 ga watan Maris na wannan shekarar da muke ciki, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ya kara bayyana ka'idar da ya kamata a tsaya a kai wajen raya zaman gurguwu mai jituwa wato ka'idar "more sakamakon da aka samu tare wajen raya zaman al'umma mai jituwa, kuma a raya zaman al'umma mai jituwa tare lokacin da ake mure sakamakon da aka samu". Ya ce, "Ya kamata a girmama muhimmin matsayin jama'a da tunaninsu na kagowa, a yi matukar kokari don himmantar da jama'a da su shiga harkokin raya kasa da kagowarsu a wannan fanni, kuma a yi iyakacin kokari domin samun tabbaci da kiyaye da kuma bunkasa babbar moriyar tarin jama'a, ta yadda za a gudanar da ayyukan bunkasa da kuma more zaman al'umma mai jituwa tare a duk tsawon lokacin raya zaman al'umma mai jituwa."

JKS za ta kira babban taron wakilanta na 17 a lokacin da aka samu nasara a gwargwado wajen raya zaman al'umma mai jituwa. Kwararru masu binciken tarihin bunkasa da kuma raya JKS sun bayyana cewa, ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya da tunanin raya zaman al'umma mai jituwa sun kara samar da tsarin sanin-ka ga sha'anin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje wanda JKS ta ba da shawarar yin sa. Shehun malami Wu Zhongfa wan da ya zo daga jami'ar kwamitin tsakiya na JKS ya bayyana cewa, "Kasar Sin ta riga ta shiga cikin wani muhimmin lokacin sauyawa, wato ta shiga cikin sabon lokacin kagowa wajen tsarin yin gyare-gyare, a daidai wannan lokaci ne za a kira babban taron wakilai na 17 na JKS".  (Umaru)


1 2