Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-27 14:15:10    
Taro na 17 na wakilan duk kasa na JKS wani taro ne na al'ada da bude wata sabuwar makoma cikin yunkurin bunkasa kasar

cri

Za a bude babban taro na 17 na wakilan duk kasa na JKS wato jam'iyyar da ke rike da mulkin kasar Sin a tsakiyar watan Oktoba mai zuwa a nan birnin Beijing. Kwararrun da abin ya shafa sun bayyana cewa, za a yi wannan babban taro ne a daidai lokacin da kasar Sin ta shiga wani muhimmin lokaci wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, an kimanta cewa, a gun wannan taro za a tattara fasahohin da J,.K.S. ta samu cikin shekaru 30 da suka wuce wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimi ga gudanar da tunanin bunkasa kasa ta hanyar kimiyya da raya zaman al'umma mai jituwa. Sakamakon taron zai jawo babban tasiri ga raya kasar Sin a nan gaba.

Shehun malami Dai Yanjun, mai binken tarihin ci gaba da kuma raya JKS ya bayyana cewa, "In an duba wannan taro, za a iya gane cewa, za a yi wannan taro ne a lokacin da aka shafe shekaru kusan 30 ana yin gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin, cikin wadannan shekaru 30 da suka wuce, an samu fasahohi masu daraja da yawa, wadanda kuma ya kamata mu tattara su cikin nitsuwa."

Ta hanyar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta samu nasarori masu jawo hankalin duniya. A sa'i daya kuma kasar Sin ta gamu da wasu matsaloli bisa hanyar samun bunkasuwa. Idan aka waiwayi tarihin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umman kasar Sin tun bayan babban taro na 16 na wakilan duk kasar Sin na JKS da aka yi a shekarar 2002 zuwa yanzu, ana iya gane cewa, bisa karuwar karfin da kasar Sin ta samu wajen tattalin arziki, matsakaicin yawan GDP wato jimlar kudin da aka samu daga aikin kawo albarkar kasa da kowane mutun kasar Sin ya samu ya riga ya wuce dalar Amurka 1,000, kuma karo na farko ne ya zarce dala 2,000 a shekarar 2006, sha'anin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da JKS ta kaddamar ya shiga cikin wani lokaci mai kyau. Ko da yake a galibai dai ana cikin zaman jituwa a kasar Sin, amma ya kasance da wasu matsalolin da suke jawo illa ga jituwar zaman al'umma.


1 2