
Ran 23 ga wata, an kammala dukkan gasannin tsakiya na kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta kasa da kasa da Hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA ta shirya a biranen kasar Sin. Kungiyoyin kasashen Jamus da Amurka da Brazil da Norway sun shiga gasa ta kusan karshe. A cikin gasa da ta kusan karshe, kungiyar Jamus za ta yi karawa da kungiyar kasar Norway, kungiyar Amurka za ta kara da kungiyar Brazil. Ana yin gasar cin kofin duniya ta wasann kwallon kafa ta mata a wannan karo a biranen Shanghai da Hangzhou da Wuhan da Chengdu da kuma Tianjin. Za ta rufe gasar a ran 30 ga wata.

Ran 17 ga wata, a nan Beijing, kwamitin shirya budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ya sanar da cewa, Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta nada 'yar wasa Zheng Jie ta kasar Sin a matsayin jakadan sa kaimi kan tabbatar da zaman daidai wa daida a tsakanin maza da mata, wadda ita ce zakara a cikin gasa ta tsakanin mata biyu biyu a cikin budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Australia a shekarar 2006. Nauyin da hukumar UNESCO ta danka wa wannan jakada shi ne yada tunanin sa kaimi kan tabbatar da zaman daidai wa daida a tsakanin maza da mata a duk duniya, da kuma shiga harkokin da hukumar za ta shirya. Zheng Jie Basinniya ce ta farko da ta sami irin wannan nadi.(Tasallah) 1 2
|