Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 14:52:45    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(20/09-26/09)

cri

Ran 21 ga wata, a nan Beijing, kakakin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya sanar da cewa, saboda da kansa ne kawai kwamitin wasan Olympic na Taipei na kasar Sin ya tsayar da shawarwari kan shiga harkar mika wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing cikin Taiwan na kasar Sin, shi ya sa a hukunce ne kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa ya tsai da kudurin soke shirin mika wa juna wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing a birnin Taipei. A ran 26 ga watan Afril na wannan shekara, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da kasafin shirin hanyar mika wa juna wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing. Bisa shirin da aka tsara, wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing za ta tashi daga birnin Beijing, hedkwatar Sin a ran 31 ga watan Maris a shekara mai zuwa, za ta ratsa birane a ketare da kuma birane da yankuna 113 a gida, za ta dawo filin wasa da za a yi bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing a daidai lokacin da za a bude wannan muhimmin gasar wasannin motsa jiki a ran 8 ga watan Agusta. A kan hanyarta, za ta ratsa birnin Taipei.

Ran 21 ga wata, a nan Beijing, an kafa kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Sin, wadda za ta shiga taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na kasa da kasa a karo na 12. Wannan kungiya ta hada da 'yan wasa 1274, za su shiga dukkan kananan wasanni 21 da kuma kananan wasanni 4 da ba domin samun lambar yabo ba. Za a yi taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na kasa da kasa a karo na 12 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin tun daga ran 2 zuwa ran 11 ga wata mai zuwa. Wannan na karo na farko da za a yi taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na duniya a Asiya kuma a wata kasa mai tasowa.


1 2