Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-25 15:44:28    
Ana iya yin amfani da salula domin kallon shirye-shiryen vidiyo

cri

Malama Yang Shan wadda take aiki a wani kamfanin kasashen waje a kasar Sin ta taba kallon wasan "magama" da salula.Idan an kwanta wasan a salula da wasannin vidiyo a telebijin,wasan nan gajere ne kuma saukakke,duk da haka yana da kyaun gani sosai,'yan wasa suna cikin sabon yayi.na ji dadin kallonsa.ta kuma gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa "A ganina abu mafi muhimmanci gare ni shi ne ina iya kallon shirye-shiryen vidiyo da salula a duk lokacin da nake jiran bus ko jirgin sama da sauransu.Ta haka kuwa ya kara wani abin jin dadi a zaman rayuwarmu."

Jama'a masu karatu,a zahiri kallon shirye-shiryen vidiyo ya riga ya zama wata hanyar da aka saba bi a wasu kasashe kamar Amurka da Japan da Korea ta kudu da kuma kasashen Turai,yana da muhimmanci a zaman yau da kullum na talakawa.A cikin wadannan kasashe,ko a dakin jiran jiragen sama,ko a gidajen cin abinci da shara,ana iya ganin mutanen dake amfani da wayar salula wajen kallon shirye-shiryen bidiyo.Mutane na iya shakatawa yayin da ba su cikin aiki.shi ya sa ya samu karbabuwa.

An fara kallon shirye-shiryen vidiyo da wayar salula ne a karshen shekarar bara a kasar Sin.Muhimmin dalili kuwa shi ne alamomi na tafiya cikin rashin sauri a giza gizan sadarwa na kasar Sin.Giza gizan sadarwa na kasar Sin ya kai matsayin biyan kallon shirye-shiryen vidiyo a karshen shekarar bara.Wani dalili kuwa shi ne irin salula da ake amfani da shi wajen kallon shirye-shirye ya fi tsada,galibi dai ya kai kudin Sin Renminbi sama da dubu biyar,wannan wani muhimmin dalili ne da ya kawo tasiri ga bunkasa harkar kallon shirye-shiryen vidiyo da salula a kasar Sin.(Ali)


1 2