Mutane ba ma kawai suna amfani da shi wajen buga waya da aikawa da sakonni da daukar hotuna da kuma adana lambar waya ba,tare da cigaban kimiyya da fasaha,ga a shi a yanzu mutane na iya amfani da shi wajen kallon shirye-shiryen vidiyo.To a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya kawo kan cigaban da aka samu a wannan fanni.
Kamfanin yada labarai na Leshi na birnin Beijing wanda ya dukufa wajen bunkasa shirye-shiryen vidiyo musamman domin wayoyin salula ya zuba jari wajen shirya wasan "magama".Babban manajan kamfanin nan Mista Liu Hong ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa "bisa ainihin halin da wayar salula ke ciki,an shirya kowane kashi na wasan da minti biyar.dalili kuwa shi ne,fuskar salula ba ta da girma,idan aka zura ido kan fuskar salula cikin dogon lokaci,ido ya kan gaji,shi ya sa aka shirya wasan na tsawon minti biyar wanda ya fi dacewa da bukatun masu kallo da salula."
1 2
|