Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 12:48:02    
Afrika tana kokarin hana a mai da ita a kan matsayin mai rakiya wajen bunkasa tattalin arziki.

cri

Na biyu,tsare tsaren raya tattalin arzikin kasashen Afrika na kara ingantuwa.Cikin yin amfani da arzutattaun albakartan da suke da su,kasashen Afrika wajen shiga da jarin ketare.Sun daidaita shirinsu na bunkasa harkar haka ma'adina,sun kuma gaggauta kafa dokoki da tsara shirye shiryen bunkasa harkar ma'adinai na matsakaicin lokaci da gajeren lokaci,sun jaddada cewa sun tsaya kan muhimman ka'idoji guda biyu wato yayin da ake bunkasa harkar ma'adinai ya kamata a kiyaye muhalli da bunkasa tattalin arziki na wuri.Daga dukkan ayyukan haka ma'adinai,hakan gurbataccen man fetur ya fi jawo hankulan mutane.Chadi da Sudan da Eqyatorial Guinea da Mauritaniya sun fi samun saurin ci gaba wajen hako man fetur.A sa'I daya kuma kasashen Afrika kuma sun sanya kokarin wajen bunkasa sadarwa,suna fatan su rage bambancin dake tsakaninsu da kasashe masu sukuni na duniya a fannin sadarwa.Ci gaban da nahiyar Afrika ta samu wajen fasahar yanar internet da wayoyin salula shaida ce a bayyane.Bisa kididdigar da hukumar sadarwa ta duniya ta yi,an ce a farkon shekarun 1990,a kasar Afrika ta kudu da Massar da kuma Tunisiya kawai na Afrika ana iya samun yanar internet,a karshen shekarun 1990 ana iya samun yanar internet a kasashe 50 na Afrika,A tsakiyar shekarun 1990,fadin filin Afrika dake da wayar salula ya dau kashi 0.06 bisa dari,a shekara ta 2004,ya kai kashi 9.1 bisa dari.Afrika ta zama nahiya daya tilo a duniya da yawan wayoyin salula ya fi wayoyin da aka girka a gidaje yawa a duniya.

Na uku,kan shirin raya kasa,kasashen Afrika sun jaddada muhimmancin samun ci gaba bisa dogaro da kansu da taimakon sauran kasashen duniya.A watan Oktoba na shekara ta 2001,shugabannin kasashen Afrika sun tsara sabon shirin abokantaka kan cigaban Afrika,wato muhimmin shiri ne na raya kasa da kuma tsarin ayyuka da suka tsara don raya kasa bisa dogaro kan kai da taimakon sauran kasashen duniya a lokacin da duniya ke cikin halin hada hadar manufofin tattalin arziki da mai da Afrika a matsayin mai rakiya.A cikin shirin nan an mai da fiffiko a fannonin horaswar kwararu da yin manyan ayyuka da aikin gona da sana'ar kerekere da kiyaye muhalli,sun tattara kudade ta hanyoyi daban daban ciki har da amfani da kudaden ajiya a bankuna da karin haraji da neman karin jari da taimakon kasashen waje da yunkurin neman rage basussukan waje.Shirin nan ya samu goyon baya daga kasashe da hukumonin duniya.Kasar Sin ta cika alkawaran da ta dauka na nuna wa Afrika goyon baya bisa shirye shiryen dandalin hadin kai tsakanin Sin da Afrika.A halin yanzu Kasar Sin ta zama wata muhimmiyar kasa da ta yi manyan ayyuka a Afrika.Za ta kuma kara taka muhimmiyar rawa wajen aikin gona da sana'ar kerekere da sauran fannoni na Afrika.(Ali)


1 2