Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 12:48:02    
Afrika tana kokarin hana a mai da ita a kan matsayin mai rakiya wajen bunkasa tattalin arziki.

cri

An yi taron shekara shekara a karo na 42 na kwamitin kungiyar bankin raya kasa na Afrika daga ran 6 zuwa ran 17 ga watan Mayu a birnin Shanghai na kasar Sin.A kan matsayin muhimmiyar hukumar kudade a Afrika,bankin raya Afrika ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Afrika da hada hada manufofinsu a fannin nan.Tun daga shekara ta 1985 da kasar Sin ta shiga kungiyar bankin raya Afrika,kasar Sin ta ba da cikakken hadin kai ga hukumar nan.Taron shekara shekara da bankin raya Afrika ya yi a kasar Sin ya shaida cewa kasashen Afrika sun dora muhimmanci kan hadin kai tsakanin Afrika da Sin. Kuma suna fatan su yi aiki tare da kasar Sin kafada da kafada wajen kara bunkasa tattalin arzikin Afrika.

A yayin da ake hada hadar manufofin tattalin arzikin duniya,an taba daukar Afrika a kan matsayin nahiya mai rakiya.Bayan da kasshen Afrika suka yi kokari cikin shekarun baya,tattalin arzikin Afrika ya samu wani ci gaba,an dakile cigaban yunkurin mai da ita a matsayin mai rakiya.

Da farko,Afrika ta kara taka muhimmiyar rawa a kan dandalin tattalin arzikin duniya.Wani rahoto kan makomar tattalin arzikin duniya da kungiyar Asusun ba da lamuni ta duniya wato IMF ta bayar a watan Afrilu na bana ya yi nuni da cewa kashin da tattalin arzikin Afrika ya dauka a cikin tattalin arzikin duniya ya kai kashi uku da digo hudu bisa dari.Idan aka yi la'kari kan kwatankwacin karin da Afrika ta samu wajen samar da kayayyaki da kashi 4.6 bisa dari a kowace shekara daga shekara ta 2000 zuwa shekara ta 2006,wanda ya zarce matsayin kwatankwacin karin da duniya ta kai,taimakon da Afrika ta bayar ga cigaban tattalin arzikin duniya ya fi yawa.A tsakanin shekara ta 2004 da shekara ta 2006,jarin da kasashen waje suka zuba kai tsaye a Afrika ya karu da kashi 26.5 bisa dari a ko wace shekara.wato ya kai dalar Amurka biliya 38.8 a shekara ta 2002 daga dalar Amurka 17.2 a shekara ta 2004.Jarin wajen da aka zuba kai tsaye a Afrika ya dau kashi 10.6 bisa dari na irin jarin da aka zuba a kasashe masu tasowa.


1 2