Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-21 16:41:21    
Kogunan kasar Sin

cri

Gabobi biyu na kogin Yangtse, wurare ne masu ni'ima, ga kyan karkara da kasa mai albarka, wurin na da arzikin amfanin gona kwarai da gaske. Gabobin biyu sun kuma kasance wurin da ke da dimbin jama'a da kuma cigaban tattalin arziki a kasar Sin. Kogin ya ratsa shahararrun birane da dama na kasar Sin, ciki har da Chongqing da Yichang da Wuchang da Nanjing da kuma Shanghai, musamman ma Shanghai, wanda birni ne mafi girma a kasar Sin a fannin masana'antu da kasuwanci. Sai kuma a fannin karfin ruwa, kogin Yangtse ya kasance kogin da aka fi samun karfin ruwa a kasar Sin, har ma karfin ruwan da yake da shi wajen samar da wutar lantarki ya kai kilowatt miliyan 200. Bayan haka, a gabobin biyu, akwai wuraren tarihi da dama, wadanda suke da daraja sosai wajen fahimtar tarihin kasar Sin.

Bayan wadannan, Sin tana kuma da sauran shahararrun koguna da yawa, misali, Rawayen kogi, wanda ya kasance babban kogi na biyu a kasar Sin, kuma tsawonsa ya kai kilomita 5,500, a yayin da fadinsa ya kai murabba'in kilomita sama da dubu 750. Rawayen kogi wuri ne da aka fara samun wayewar kan al'ummar kasar Sin, tun shekaru aru-aru da suka wuce ne, sai kakanin kakanin Sinawa suka fara farauta da ayyukan gona da kuma zaman rayuwarsu a gabobin kogin. Kogin alama ce ta al'ummar kasar Sin, shi ya sa ake kiranta "kogin mahaifa" ta al'ummar kasar Sin.

Sai kuma kogin Pearl wanda ya taso daga lardin Yunnan na kasar Sin, sa'an nan ya malala ya ketare lardunan Yunnan da Guizhou da Guangxi da kuma Guangdong na kasar, daga karshe ya shiga cikin tekun kudu, wannan ya kasance kogi mafi girma a kudancin kasar Sin.

A kasar Sin, akwai kuma koramu da yawa da Sinawa suka yi, musamman ma koramar Jinghang wadda ita ce korama mafi dadadden tarihi kuma mafi tsawo da dan Adam ya yi a duniya. Koramar dai ta hada birnin Beijing da ke arewa da kuma birnin Hangzhou da ke kudu, kuma tsawonta ya kai kilomita 1801. koramar tana da tsawon tarihi na shekaru fiye da 2,000, kuma ta shahara ne daidai kamar babbar ganuwar Sin. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, an yi mata gyara, har zuwa yanzu dai, tana taka muhimmiyar rawa a wajen sufuri da ban ruwa da magance ambaliyar ruwa da dai sauransu.(Lubabatu)


1 2