Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-21 16:41:21    
Kogunan kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Alhaji Abubakar Umaru, mazaunin birnin Abuja da ke tarayyar Nijeriya. A cikin sakon da malam Abubakar Umaru ya turo mana, ya ce, kogin Yangtse wani shahararren kogi ne a kasar Sin, kai har ma a duniya baki daya, sashen Hausa na rediyon kasar Sin, ina so ku ba ni labarin kogin. Ban da kogin Yangtse, ko akwai sauran koguna a kasar Sin?

A hakika, Sin tana daya daga cikin kasashen duniya da suka fi samun koguna. A nan kasar, akwai manyan koguna da dama, kuma daga cikinsu, yawan kogunan da fadinsu ya wuce muraba'in kilomita 1,000 ya kai sama da 1,500.

Game da shahararren kogin nan da ake kira "Yangtse", tsawonsa ya kai kilomita 6,300, kuma kogin ya kasance babban kogi na farko na kasar Sin kuma kogi mafi tsawo a nahiyar Asiya, kai har ma babban kogi na uku a duniya, wato bayan kogin Nile da ke nahiyar Afirka da kuma kogin Amazon da ke Amurka ta kudu. Kogin ya taso daga dutsen Geladaindong da ke Platon Qinghai-Tibet da ke yammacin kasar Sin, sa'an nan kogin ya karkata zuwa gabas, ya yi ta kwarara, har ya ratsa lardunan Qinghai da Sichuan da Tibet da Yunnan da Chongqing da Hubei da Hunan da Jiangxi da Anhui da Jiangsu da kuma birnin Shanghai na kasar Sin, wadanda suka kai 11 gaba daya, daga karshe dai, ya malala cikin tekun gabas. Fadin kogin Yangtse ya kai murabba'in kilomita sama da miliyan 1 da dubu 800, wanda ya dau kimanin kashi daya daga cikin biyar na fadin kasar Sin gaba daya.

1 2