Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-20 18:24:35    
Jama'ar kasar Sin suna jiran babban taron wakilan JKS

cri

Shehu malama Chen Xuewei ta jaddada cewa, bayan babban taro na karo na 16 na jam'iyyar kwaminis ta duk kasar Sin da aka yi a shekarar 2002, karfin daidaita batutuwan da suke da nasaba da zaman rayuwar farar hula yana ta karfafuwa.

Mr. Yi Xianrong wanda ya kware kan ilmin tattalin arziki na kasar Sin ya bayyana cewa, ko da yake za a bayar da sabbin takardu da manufofi da matakai na mulkin kasar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta dauka a gun babban taro na karo 17 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta duk kasar Sin. Amma ana ta bayar da wasu manufofi daga cikinsu ko kuma ana tsara su. A matsayin wani masanin ilmin tattalin arziki, Mr. Yi Xianrong yana fatan wannan babban taro zai sa kaimi ga kokarin raya kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin yadda ya kamata domin moriyar farar hula. Mr. Yi ya ce, "Ya kamata a ce, a cikin shekaru 5 da suka wuce, muhimman matsaloli biyu da suke kasancewa a kasuwannin cinikin gidaje da hada-hadar kudi su ne farashinsu ba su iya bayyana hakikanin halin da ake ciki a kasar. Idan za a a iya daidaita wadannan matsaloli a gun babban taro na karo 17 na jam'iyyar, za a iya mayar da farashinsu kamar yadda ya kamata. tattalin arziki zai iya samun cigaba mai dorewa." (Sanusi Chen)


1 2