Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-20 18:24:35    
Jama'ar kasar Sin suna jiran babban taron wakilan JKS

cri

A watan Oktoba mai zuwa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da ragamar mulkin kasar Sin za ta kira babban taro na karo na 17 na wakilanta na duk kasar. Wannan wani muhimmin taro ne da za a kira lokacin da aikin gyare-gyare da neman bunkasuwar kasar Sin take shiga muhimmin mataki. Wannan taro zai taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga al'ummomin duk kasar Sin da dukkan membobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da su kara yin kokarin raya zaman al'ummar gurguzu ta zamani da ke bayyana halin musamman da kasar Sin ke ciki. A cikin 'yan kwanakin nan, lokacin da wakilanmu suke neman labaru, jama'a wadanda suke aiki a fannoni daban-dabam suna jiran wannan babban taro. Suna fatan wannan taro zai kawo wa jama'a karin moriya.

Madam Chen Fan, wata mazauna ce ta birnin Beijing. Maganar da ta fadi tana wakiltar abubuwan da mutane wadanda suke jiran wannan taro suke jira. "Muna fatan wakilan jam'iyyar za su iya tattaunawa batutuwan da suke da nasaba da zaman rayuwar farar hula. Alal misali, batun neman aikin yi da yake kasancewa a gaban dalibai wadanda za su gama karatu daga jami'o'i da batun farashin gidaje da batun da yake nasaba da lafiyar farar hula da dai makamatansu. Farar hula suna fatan wannan babban taro zai kawo musu moriya ta hakika."

Kamar madam Chen Fan ta fadi, yanzu farar hula na kasar Sin suna fuskantar matsaloli 3, kamar su gidaje masu tsada da shigar da yara cikin makaranta da magunguna masu tsada.

Madam Chen Xuewei, shehu malamar makarantar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta bayyana cewa, babban taro na karo na 17 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta duk kasar Sin muhimmin abu ne mai kyau ga farar hula domin wannan taro zai kawo musu hakikanan abubuwa da yawa bayan da aka samu cigaban tattalin arzikin kasar Sin. Wannan taro zai zama sabon mafari ne ga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da ragamar mulkin kasar. Kuma zai kara kawo wa farar hula fatan alheri. Mr. Yi ya ce, "A gun taron, wakilai za su tattauna kan tsarin raya kasar Sin na tsawon shekaru 8 ko shekaru 13 masu zuwa. Bugu da kari kuma, za a kara tabbatar da wasu muhimman ayyukan yin gyare-gyare da neman cigaba da za a yi a cikin 'yan shekaru masu zuwa. Wadannan muhimman ayyuka shi ne, raya sabon kauyuka da canza hanyar raya tattalin arziki. Dole ne mu canza hanyar neman bunkasuwa cikin sauri, amma muna samun moriya kadan, kuma mun zuba kudade da abubuwa da yawa, amma ba mu samu sakamakon da muke bukata ba. A waje daya, mu nemi wata sabuwar hanyar neman bunkasuwa, wato dan Adam da halittu za su kasance tare cikin jituwa, kuma zaman al'umma da tattalin arziki za su iya samun cigaba cikin halin daidaito, kauyuka da birane za su iya samun bunkasuwa tare da dai sauransu."

1 2