Likita Messias ya yi hasashen cewa, bisa wanann binciken da aka gudanar, an gano cewa, mutane da yawa suna bukatar a yi musu jiyya wajen lafiyar tunani, amma kullum rashin kula da wadannan cututtuka. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wasu mutane suna ganin cewa, ana iya warkar da cututtukan tunani da kansu, kuma ba a bukatar ganin likita. Wasu mutane kuwa suna ganin cewa, ba a iya warkar da cututtukan tunani kwata kwata ba, ban da wannan kuma wasu mutanen da suke fama da cututtukan ba su son ganin likita domin matsin lamba da suka samu daga zaman al'umma ko kuma domin kiyaye martabobinsu. Bugu da kari kuma wasu cututtukan tunani ba su cikin inshorar jiyya, da kuma karancin likitoci masu kula da lafiyar tunani su ma muhimman dalilai ne. manazarta suna ganin cewa, ba tilas ba ne a bukaci shan magunguna wajen warkar da cututtukan tunani, za a iya saussauta cututtukan ta hanyar yin amfani da hankalin mutane.
Ban da wannan kuma binciken ya gano cewa, kullum a kan amince da yi wa wadanda suka kamu da cutar rashin hankali jiyya, amma kullum ana rashin kula da cututtukan tunani marasa tsanani ba. A fannin lafiyar jama'a, cututtukan rashin hankali suna iya yin illa ga wasu mutane kawai, amma matsalolin lafiyar tunani za su shafe mutane mafi yawa. Sabo da haka kwararuu sun yi kira da a horar da likitoci musamman wajen kula da lafiyar tunani domin biyan bukatun mutane masu yawa.(Kande) 1 2
|