Kwararrun kasar Amurka wajen cututtukan tunani sun gudanar da wani bincike ga fararen hula wajen lafiyar tunaninsu, kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, 'yan Amurka da yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin dari suna fama da cututtukan tunani iri daban daban, amma sulusin daga cikinsu ne kawai suka je asibiti wajen ganin likita. Sabo da haka kwararru sun yi kira ga dan Adam da su kula da lafiyar tunani, muddin sun kamu da cututtukan tunani, ya kamata su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin likita.
Kungiyar bincike da ke karkashin jagorancin likita Eric Messias na kwalejin ilmin likitancin na jihar Georgia na kasar Amurka ta ba da rahoton, cewa sun gudanar da wani bincike ga mutane 816 na birnin Baltimore na jihar Maryland na Amurka daga shekara ta 1993 zuwa shekara ta 1999. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, a cikin cututtukan tunani iri daban daban da suke bukatar warkarwa, mutanen da suke fama da cutar dogaro da giya su ne mafi yawa, wato ya kai kashi 14 cikin dari, na biyu shi ne mutanen da suke fama da cutar bakin ciki, wato ya kai wajen kashi 11 cikin dari. Ban da wannan kuma mutane masu yawa suna kamuwa da cutar jin tsoro da cutar tsoron yin mu'amala da sauran mutane.
1 2
|