Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-19 08:37:10    
Ana yin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007 a birnin Shanghai na kasar Sin

cri

A halin da ake ciki yanzu,matsayi da karfin tasiri na wasan kwallon kafa na mata sun riga suna dada daguwa bisa babban mataki,ban da wannan kuma,a karkashin kokarin da kwamitin shirya gasar na kasar Sin da babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya suka yi tare,gasar nan ta ba mu mamaki sau tarin yawa.Alal misali,ana iya kallon gasar a kasashe da shiyoyyi fiye da dari biyu a duk fadin duniya,amma a da ba haka ba ne,kuma,manema labaru fiye da dubu daya da dari tara suna watsa labaran gasar.Ban da wannan kuma,za a bai wa kungiyoyi masu halartar gasar kudin yabo da yawansa zai kai kudin dalar Amurka miliyan shida da dubu dari hudu.wato a kalla kowace kungiya za ta samu kudin dalar Amurka dubu 250,kungiyar da ta samu zama ta farko za ta samu kudin dalar Amurka miliyan daya.Kazalika,ana tafiyar da ayyukan karbar `yan wasa da sauran mutanen da abin ya shafa lami lafiya.

Game da wannan,mataimakiyar shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin kuma babbar sakatariyar zartaswa ta kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta mata ta shekarar 2007 Xue Li ta bayyana cewa,  `Muna fatan wannan gasa za ta zama babbar salla ga masu sha`awar wasan kwallon kafa,kuma muna fatan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007 za ta ci cikakkiyar nasara.`

Yanzu dai,kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata daban daban suna yin takara mai tsanani,kafin karshen wannan wata,masu sha`awar wasan kwallon kafa suna iya jin dadin kallon gasannin ta gidajen TV tare.To,wa za ta samu zama ta farko,bari mu sa ido mu gani.(Jamila Zhou)


1 2