Ran 10 ga wata da dare,a birnin Shanghai na kasar Sin,an yi gaggarumin bikin bude gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007,wannan gasa ita ce gasar wasan kwallon kafa mafi muhimmanci da babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya ta shirya a wannan shekara.Za a yi gasar nan a birane biyar na kasar Sin wadanda ke hada da Shanghai da Hangzhou da Chengdu da Wuhan da kuma Tianjing.Daga ran 10 zuwa ran 30 ga wannan wata,kungiyoyin `yan wasa masu karfi 16 da suka zo daga wurare daban daban na duk fadin duniya za su yi takara mai tsanani domin neman samun zakarar wasan kwallon kafa ta matan duniya.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.
An yi bikin bude gasar nan a filin wasan motsa jiki na Hongkou na shanghai,babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya da kwamitin shirya gasa na kasar Sin sun samar da wani taron wake-wake da raye-raye ga `yan kallo,babban batun taron shi ne `karfin wasa yana da kyan gani sosai`.`Yan wasan fasaha sun nuna mana cewa,`yan wasan kwallon kafa mata su ne kyakkyawa.To,ga waka mai taken `yarinya da kwallon kafa` da shahararriyar zabiyar kasar Sin Wei Wei ta rera.
Daga baya kuma,shugaban babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya Joseph S.Blatter ya mika wa Sun Wen tsohuwar shahararriyar `yar wasan kwallon kafa ta duniya kuma tsohuwar `yar wasan kwallon kafa ta kasar Sin wani kwallo wanda ke da alamar bunkasuwar wasan kwallon kafa na mata a cikin shekaru 16 da suka wuce wato tun bayan da aka soma gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata,kuma ya sanar da budewar gasar cin kofin duniya ta mata ta shekarar 2007.Ya ce: `Yanzu,ina jin dadi,bari in sanar da cewa,gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007 ta fara a hukunce.`
An soma gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata a shekarar 1991,an saba shirya gasar sau daya a duk shekaru 4,gasar bana ita ce ta zama ta biyar.A shekarar 1991,an taba shirya gasa ta farko a birnin Guangzhou na kasar Sin,wato wannan shi ne karo na biyu da kasar Sin ta shirya gasar.Saboda haka,shugaba Blatter ya ce: `Kasar Sin wurin masomi ce na wasan kwallon kafa,an fara wasan ne a kasar Sin kafin shekaru fiye da dubu biyu da suka shige.Yanzu ana yin gasar cin kofin duniya a kasar Sin wato garin wasan kwallon kafa,muna jin dadi .`
1 2
|