
Dadin dadawa kuma, an nuna kyawawan mutum-mutumi masu daraja da aka yi a zamanin daular Beiwei da na Tang na kasar Sin wato a tsakanin shekarar 386 zuwa ta 534 da kuma a tsakanin shekarar 618 zuwa ta 907 a cikin dakin nune-nune a gidan ibada na Yufo. Baya ga wadannan mutum-mutumi kuma, an ajiye littattafan addinin Buddha da zane-zane da aka waiwaya da hannu a zamanin daular Tang na kasar Sin.
'Yan addinin Buddha fiye da 70 su kan yi ayyukan yau da kullum a gidan ibada na Yufo. Ban da wannan kuma, in masu yawon shakatawa sun ji yunwa a lokacin da suke ziyara a gidan ibada na Yufo, to, wani dakin cin abinci da wannan gidan ibada ke tafiyar da shi yana iya samar da ire iren abinci masu dadin ci. Wannan dakin cin abinci ya ji alfahari sosai saboda yana samar da dukkan abinci da kayayyakin lambu da Tofu, ko da yake sunayen wadannan abinci suna shafar nama da kifi da nama kaji da naman agwagi. 1 2
|