Gidan ibada na addinin Buddha na Yufo da ke birnin Shanghai aka gina shi a sheakar 1882. Ma'anar Yufo a Sinance ita ce mutum-mutumin Buddha da aka yi da lu'ulu'u irin na jade. Bayan da aka yi juyin mulki a shekarar 1911, an kyale shi, ba a kula da shi yadda ya kamata ba, shi ya sa a tsakanin shekarar 1918 zuwa shekarar 1928 an sake gina shi a wurin da muka gani a yau.
Mutum-mutumin Buddha 2 na lu'ulu'u da ke cikin wannan gidan ibada su ne wasu 2 daga cikin dukkan mutum-mutumin Buddha guda 5 na lu'ulu'u da dan addinin Buddha Huigen na babban tsaunin Putuo ya kawo daga kasar Burma wato kasar Myanmar ta yanzu a shekarar 1882. An taba ajiye su a bayan gari na birnin Shanghai a farko.
Gidan ibada na Yufo ya hada da manyan zaunuka guda 3, wato babban zauren na Maitreya, da babban zauren Daxiongbaodian da kuma babban zauren Sanshengdian. A cikin babban zauren Maitreya, an ajiye mutum-mutumin Buddha mai suna Maitreya wato Buddha da ke kan murmushi. A cikin babban zauren Daxiongbaodian, wato babban bangare na gidan ibada na Yufo, an ajiye mutum-mutumin Sakyamuni tare da mabiyansa 2 a dab da shi, wadanda ya fi so, wato Ananda da kuma Kasyapa.
A cikin babban zauren Yufo, akwai wani mutum-mutumi mai tsayin misalin mita 1.9 na Sakyamuni da aka kera da lu'ulu'un jade. Sakyamuni, wanda ya kafa addinin Buddha, ya zauna a nan cikin lumana. Sa'an nan kuma, in masu yawon shakatawa sun kawo ziyara a babban zauren Wofo, suna iya ganin wani kwantaccen mutum-mutumin Sakyamuni, wanda aka kera da lu'ulu'un jade mai launin fari, tsawonsa ya kai misalin santimita 96. Ma'anar Wofo a Sinance ita ce Buddha da ke kwanta.
1 2
|