Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-18 16:49:50    
Wakilin rediyon kasar Sin ya kai ziyara a birnin Tian Jin dake bakin teku na arewancin kasar Sin

cri

Bayan da aka yi gine gine har cikin shekaru fiye da 100 da suka shige, birnin Tain Jin ya riga ya zama wani birni mai wadata sosai. Amma tarihi na wannan birni yana nan yana ci gaba da kasancewa.

In ka so neman sanin birnin Tian Jin ya kamata da farko bari mu je tsohon birnin Tian Jin, Tsohon birnin Tian Jin yana cibiyar wannan birni, tun a da har zuwa yanzu, 'yan kasuwa suna son cunkushe a nan, wato an kasance da wurin arziki sosai, wannan wuri shi ne cibiyar yin siyasa da tattalin arziki da al'adu. A nan akwai manyan kantunan da aka gina, a nan ka iya yin saye saye da nishadi, A nan kuma an kebe hanyoyin da aka hana motocin da suka ratsa wurin, wato mutane suna yin yawo suna saye saye har suna jin dadi ba tare da tsoron ratsawar motoci ba.

Wani tsoho mai suna Wang zhen dong yana da shekaru fiye da 70 da haihuwa, ya gaya wa wakilin rediyonmu cewa, wani babban gini mai bene da yawa wato kamar husumiya shi ne tsohon abin shaida na tarihin birnin Tian Jin, wanda yana da tsawon tarihi fiye da shekaru 600, Wato wannan babban gini ya iya jawo tunanin jama'a da su waiwayo tarihin birnin Tian Jin. Ya kuma gaya mana cewa, har yanzu dai manyan dakunan ibada da manyan bankunan da lambunan shan iska da 'yan kasuwa na kasashen waje suka gina suna kasancewa da kyau.

In ka zo birnin Tian jin don yin shakatawa ban da abubuwan dake cikin birnin Tain Jin, ga kyakyawan halitta na birnin Tian Jin ita ma tana jawo masu yawon shakatawa na gida da na kasashen waje, Wani babban tudu mai suna Pan shan shahararren wuri mai ni'ima sosai dake kusa da birnin Tian Jin


1 2