Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-18 16:31:36    
Bayani kan yadda ya kamata a yi watsi da shan taba

cri

Nazarin kimiyya ya bayyana cewa, taba za ta iya haifar da munanan illoli iri fiye da 4000 idan aka kuuna ta, kuma wadanda su kan sha taba suna iya kamuwa da ciwon kansa da na zuciya da hauhawar jini da dai sauransu. A ko wace shekara, mutane kusan miliyan biyar ne suke mutuwa sakamakon ciwace-ciwacen da ke da nasaba da shan taba. Wadanda suka saba da shan taba da yawa suna son yin watsi da ita, amma kadan daga cikinsu ne suna cin nasara, yayin da yawancinsu ba su iya ba. Ko akwai dabaru masu kyau kan yin watsi da shan taba? To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda ya kamata a yi watsi da shan taba.

Ya zuwa yanzu, a cikin masu shan taba da yawansu ya kai biliyan 1.1 a duk duniya, rabinsu suna so su yi watsi da shan taba. Amma mene ne muhimman abubuwa idan ana so yin watsi da shan taba? Madam Yang Gonghuan, shahararriyar kwararriya ce a kan kiwon lafiyar jama'a kuma mataimakiyar shugaban cibiyar magance da kuma shawo kan cututtuka ta kasar Sin ta bayyana cewa, "idan ana so a yi watsi da shan taba, da farko ya kamata ya sa niyya, kuma dole ne mutanen da ke kewaye da shi za su nuna masa goyon baya. Amma game da wadanda suka dade suna shan taba, suna bukatar magunguna a wasu lokuta. Shi ya sa muhimman abubuwa kan yin watsi da shan taba su ne niyya da muhalli da kuma magunguna."

Kamar yadda Madam Yang ta fada, akwai muhimman abubuwa uku wajen yin watsi da shan taba. To, da farko, bari mu yi managa kan niyya. Idan ana so a tsai da yin watsi da shan taba, to dole ne ya fahimci mumunar rawa da shan taba ya taka ga lafiyar jiki. Wata 'yar birnin Beijing mai suna Li Guizhen ta gaya mana cewa, "shan taba bai ba da taimako ga lafiyar jiki ba, yanzu ni wata tsohuwa ce, idan na yi tari, majina da na tofa tana da launin baki."

1 2