Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 20:20:46    
Sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin masu aikin injiniya a shirye suke, za su tashi zuwa Darfur ta Sudan

cri

Har kullum, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a kan batun shiyyar Darfur ta kasar Sudan. Tura sojojin kiyaye zaman lafiya masu aikin injiniya zuwa Darfur da gwmanatin Sin za ta yi bisa gayyatar Majalisar Dinkin Duniya a wannan karo wani muhimmin mataki ne daban da ta dauka don taimakawa Sudan wajen daidaita batun Darfur. Wadannan sojoji maza matasa za su yi wannan aiki a madadin kasar Sin.

Kafin su tashi zuwa shiyyar Darfur, an horar da sojojin wannan runduna a tsanake a fannonin karfin jiki da ayyuka da tunani da dai sauransu. Babban kanar Dai ya ce,'Ofishinmu ya shirya kos din ga kusoshin wannan rundunar soja. Bisa sigar musamman ta shiyyar Darfur da kuma hakikanan bukatun da sojoji masu aikin injiniya suke bayar, mun horar da su a fannonin tsaron lafiyar mutane, da ka'idojin yin yaki da ka'idojin halayen sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da yin mu'amala a tsakanin al'adu daban daban da kuma ci gaban halin da ake ciki a wuraren da suke kiyaye zaman lafiya da tabbatar da lafiyar mutane ta fuskar tunani da dai sauransu.'

Ban da wannan kuma, dukkan injunan da wannan rundunar soja za su tashi tare da su masana'antun kasar Sin ne suka kera su, wadanda bayan da aka yi musu bincike a tsanake, sai a fara aiki da su. Wadannan injuna na biyan bukatun sojoji masu aikin injiniya a fannonin tafiyar da ayyuka da zaman yau da kullum.

Saboda za su tafiyar da ayyuka a ketare nan gaba ba da jimawa ba, wadannan matasan kasar Sin sun ji zumudi sosai, haka kuma sun yi juyayi. Ko da yake za su tafiyar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a madadin kasar sin, amma mai yiwuwa ne halin da ake ciki a Darfur da ba su sani ba zai kawo musu dimbin wahalhalu, wadanda ba su kiyasta ba. Amma duk da haka, mawuyancin hali ba zai tsorata da sojojin kasar Sin ba. Shugaba Lin Hong na wannan rundunar soja ya bayyana ra'ayinsa a madadin dukkan sojojin cewa,'Bisa nauyin da Majalisar Dinkin Duniya ta danka mana, za mu tabbatar da gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata da samun cikakkiyar nasarar kammala wadannan ayyuka. Za mu ba da karin sabuwar gudummowa wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a Darfur ta Sudan da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'ar Sin.'(Tasallah)


1 2