Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 20:20:46    
Sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin masu aikin injiniya a shirye suke, za su tashi zuwa Darfur ta Sudan

cri

Kasar Sin za ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya 315 masu aikin injiniya zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan a farkon wata mai zuwa, bisa gayyatar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata. Yanzu wannan rundunar soja ta riga ta kammala aikin horo a tsakiyar kasar Sin, a shirye suke. A kwanan baya, wakilinmu ya zanta da rundunar.

A ran 15 ga wata, manema labaru fiye da 60 na kafofin yada labaru 35 na wurare daban daban na duniya sun je gundumar Qinyang da ke da nisan kilomita milisan 130 a tsakaninta da birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan a arewa maso yamma don kallon aikin horo da sojojin suka yi. Tun daga kwanaki 10 na tsakiya na watan Yuni har zuwa yanzu, wadannan sojoji sun yi watanni fiye da 3 suna samun horo a Qinyang.

Babban kanar Dai Shaoan, mataimakin darektan ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya gaya wa manema labaru cewa, za a fara jibge wannan rundunar sojan kasar Sin a Darfur ta Sudan a farkon watan gobe bisa bukatar Majalisar Dinkin Duniya. Za ta dauki nauyin ba da tabbacin guzuri, za ta share fage ga rundunar sojojin hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka da za a tura zuwa Darfur a fannoni daban daban.

1 2