Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 17:52:23    
Kasar Sin na mayar da hankali sosai ga ingancin abinci

cri

Bayan haka ya ba da misali cewa, kafin ma'aikatan kamfaninsa su shiga cikin wurin aikin zuba abin sha cikin kwalabe, an bukace su da su tsabce jikunansu da babu kwayoyin cuta a kai, daidai kamar yadda likitoci ke yi kafin su shiga cikin dakin yin fida. Ana yin haka duk domin tabbatar da ingancin abin sha.

A kwanakin baya, gwamnatin kasar Sin ta bayar da takardar bayaninta a kan "al'amuran ingancin abinci na kasar Sin". Malam Luo Yunbo, shugaban kolejin kimiyya da fasahar abinci na jami'ar koyon aikin noma ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta bayar da wannan takardar bayaninta ne don sa jama'ar kasa da su fahimci halin da ake ciki a kasar dangane da ingancin abinci a fannoni daban daban, wannan ya nuna cewa, kasar Sin tana sauke nauyi da ke bisa wuyanta. Ya kara da cewa, "kasar Sin babbar kasa ce da ke samar da abinci mai dimbin yawa, da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje. Sabo da haka ingancin abincinta ya jawo hankulan bangarori daban daban. A cikin irin wannan hali ne, aka bayar da takardar bayanin gwamnatin kasar Sin cikin lokaci don bayyana halin ingancin abinci na kasar, sa'an nan an bayyana wasu matakai da kasar ta dauka wajen kula da ingancin abinci, wannan ma matsayi ne da kasar ta dauka na sauke nauyin da ke bisa wuyanta."

Bisa matsayinta na wata babbar kasa da ke yin cinikayyar waje, kasar Sin tana son hadin kai da kasashe daban daban, domin inganta ma'amala da hadin kai, su yi kokari ba tare da kasala ba wajen kula da ingancin abinci da sa kaimi ga bunkasa cinikayyar abinci yadda ya kamata a duk duniya. (Halilu)


1 2