Samar da abinci mai inganci wani batu ne da ke jawo hankulan jama'ar duk duniya, don haka kullum kasar Sin tana mai da hankali sosai ga ingancin abinci. Gwamnatin kasar Sin da masana'antunta sun nuna himma sosai wajen daukar matakai iri-iri don ba da tabbaci ga samar da abinci mai inganci.
Babbar hukumar kula da harkokin dudduba ingancin kayayyaki da sanya ido da binciken cututtuka ta kasar Sin tana daya daga cikin hukumomin kula da ingancin abinci a kasar. Babban aikinta shi ne kula da ingancin abinci yayin da ake sarrafa su da kuma sanya ido kan kiwon lafiyar yau da kullum. A gun wani taron manema labaru da aka shirya a kwanakin baya dangane da harkokin ingancin kayayyaki da na abinci na kasar Sin, Malam Li Changjiang, shugaban hukumar ya bayyana cewa, "a ganina, kasar Sin tana kara kyautata ingancin abinci da kayayyaki. Daga binciken da muka yi a kan abincin kasar, mun gano cewa, yawan abinci da suka dace da ma'aunin ingancinsu ya kai kashi 85.1 cikin dari. Daga cikinsu, akwai wasu abinci mai muhimmanci masu dacewa da ma'aunin inganci kamar shinkafa da fulawa da man girki wadanda jama'a ke bukatarsu yau da kullum sun kai kashi 91.5 cikin dari. Haka kuma wasu abubuwan sha kamar ruwan lemo wadanda suka dace da ma'aunin ingancinsu ma sun riga sun kai kashi 97.5 cikin dari, kamata ya yi a ce, sun yi yawa."
Malam Li Changjiang ya kara da cewa, a cikin shekaru da yawa da suka wuce, an riga an kafa dokoki kan samar da abinci mai inganci a kasar Sin. Haka kuma an kafa tsarin kula da harkokin ingancin abinci a kasar. Kamfani mai suna "Huiyuan" na kasar Sin wani babban kamfani ne na yin ruwan lemo da sauran abubuwan sha ne. Kamfanin yana fitar da abubuwan sha zuwa kasashen Amurka da Australiya da New Zealand da sauran kasashe da shiyyoyi sama da 20 na Afrika da Asiya ta kudu maso gabas. Malam Zhu Xinli, shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin ya bayyana cewa, ingancin kayayyaki yana da muhimmanci sosai ga kamfaninsa. Ya ce, "idan wani kamfani ba ya mai da hankali sosai ga ingancin abinci da na kayayyaki ba, to, ba zai dade ba. Sabo da haka ingancin kayayyaki rayuwar kamfani ne."
1 2
|