Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-14 15:20:26    
Yankunan kasar Sin

cri

A bayanin da muka yi dazun nan, mun ambaci yankuna masu cin gashin kansu da kananan yankuna masu cin gashin kansu, watakila akwai masu karatu da ba su gane ma'anarsu sosai ba, to, yanzu bari mu kara muku bayani a kansu. Su wadannan yankuna masu cin gashin kansu da kananan yankuna masu cin gashin kansu da kuma gundumomi masu cin gashin kansu, mazaunai ne na 'yan kananan kabilun kasar Sin, kuma a wuraren, ana tafiyar da tsarin cin gashin kansu, wato 'yan kananan kabilu su ne suke tafiyar da harkokin kansu bisa ka'idojin tsarin mulkin kasar Sin. Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, gaba daya ne aka kafa yankuna masu cin gashin kansu biyar a nan kasar, wadanda suka hada da yanki mai cin gashin kansa na Mongoliya ta gida da yanki mai cin gashin kansa na Xinjiang na kabilar Uygur da yanki mai cin gashin kansa na Guangxi na kabilar Zhuang da yanki mai cin gashin kansa na Ningxia na kabilar Hui da kuma yanki mai cin gashin kansa a Tibet.

Sai kuma biranen da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye da muka ambata a baya, su manyan birane ne da ke da muhimmanci a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu, kuma majalisar gudanarwa ta kasar Sin ita ce take kula da su kai tsaye. Ya zuwa watan Maris na shekarar 1997, wato lokacin da aka mayar da birnin Chongqing na kasar Sin a matsayin birnin da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiyar kasar kai tsaye, gaba daya ne akwai irin wadannan biranen da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye guda hudu. Su ne Beijing da Tianjin da Shanghai da kuma Chongqing. Daga cikinsu, birnin Beijing, babban birni ne na kasar Sin, haka kuma cibiyar siyasa ce ta kasar, wanda kuma ya kasance cibiyar al'adu da kimiyya da kuma mahadar hanyoyi a kasar Sin. Sai kuma birnin Shanghai, wanda ke mashigin Teku na kogin Yangtse, kasancewarsa muhimmin birni na masana'antu da kuma tashar jiragen ruwa, birnin Shanghai na da muhimmanci sosai ga tattalin arzikin kasar Sin. Sai kuma birnin Tianjin, wanda ya kasance muhimmin birni na masana'antu da kasuwanci da ke arewacin kasar Sin, haka kuma wata tashar jiragen ruwa da ke da muhimmanci sosai a wajen sufurin teku da kuma cinikin da ke tsakanin Sin da kasashen waje. Ban da wadannan, birnin Chongqing cibiyar masana'antu da kasuwanci ce mafi girma a kudu maso yammacin kasar Sin.

Bayan haka, domin aiwatar da tsarin kasa daya amma tsarin mulki guda biyu, Sin ta kuma kafa yankunan mulki na musamman, wadanda ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye. Ya zuwa lokacin da aka komo da Macao a karkashin mulkin gwamnatin kasar Sin a watan Disamba na shekarar 1999, gaba daya ne Sin ta kafa irin yankunan mulki na musamman guda biyu, wato su ne Hongkong da Macao.(Lubabatu)


1 2