Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Rabe Mamane, mazaunin birnin Yamai da ke jamhuriyar Nijer, wanda ke sauraronmu a kullum. Malam Rabe Mamane ya rubuto mana cewa, ma'aikatan sashen hausa na radiyon kasar Sin, ina so ku gaya mini kasar Sin yanki nawa da lardi nawa ne gare ta da kuma gundumomi nawa?
Masu karatu, kamar yadda sauran kasashe ke yi, domin saukin tafiyar da harkokin mulki, Sin ita ma ta kafa wani tsari na rarraba yankunanta. A kasar Sin, an rarraba yankunan kasar bisa matakai daban daban, misali, a mataki na farko, akwai larduna da yankuna masu cin gashin kansu da kuma biranen da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye. Sa'an nan, a mataki na biyu, wato a karkashin shugabancin wadannan larduna ko kuma yankuna masu cin gashin kansu, akwai kuma kananan yankuna masu cin gashin kansu da gundumomi da kuma birane. Sai kuma a mataki na uku, wato a karkashin shugabancin gundumomi, akwai garuruwa. Yanzu a kasar Sin, akwai larduna 23 da yankuna masu cin gashin kansu 5 da birane 4 da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye da kuma yankunan mulki na musamman guda biyu. Bayan haka, ya zuwa karshen shekarar 2001, yawan biranen Sin ya riga ya kai 662.`
1 2
|