Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-13 13:37:47    
Me ya sa Mr. Putin ya wargaza gwamnatin Rasha?

cri

Victor Zubkov

A hakika, bayan Mr. fladkov ya yi murabus daga mukaminsa shi ma ya bayyana cewa, ya yi haka ne daidai sabili da babban al'amarin siyasa zai faru a nan gaba kadan a kasar Rasha, gwamnati tana son kawo sauki ga shugaban kasa don ya samun sharadi sosai wajen daidaita matsalar tubewa da nadawa.

Mr. Zhang bai yi mamaki sosai ba game da murabus da gwamnatin Fladkov ta yi ba zata, ya bayyana cewa, yau da shekaru 3 da suka wuce, domin share fage ga yin garambawul din gwamnati, Mr. Putin shi ma ya taba yin shelar wargaza gwamnati kafin babban zaben shugaban kasar. Amma sauye-sauyen gwamnati da aka yi har sau 2 ya kasance da kamanci sosai a tsakaaninsu. Ya ce, "A shekara 2004 wato sauran makonni 3 da Mr. Putin ya ci zaben zama shugaban kasa na karo na 2, ya wargaza gwamnatin Mikhailovich Kasyanov, kuma ya nada gwamnatin Fladkov. A lokacin kuwa Mr. Putin ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya yi haka duk domin biyan bukatar da aka yi wajen siyasa da kuma zaben shugaban kasa."

Mr. Zhang ya bayyana cewa, ta hanyar wargaza gwamnatin Fladkov, a kalla Mr. Putin zai iya cim ma wadannan makasudansa haka, "Da farko, ya kamata Rasha ta kaddamar da wasu sabbin matakai wajen gudanar da harkokin gwamnatin kasar. Na 2, sabuwar gwamnatin da za a kafa za ta iya bayyana burin yawancin mambobi masu nuna goyon baya ga shugaban kasa da ke cikin majalisar. Na 3, Mr. Putin ya za bi wannan lokaci don canja firayim ministan gwamnati zai iya ba wa jama'a masu yin zabe da zaman al'ummar Rasha wata sabuwar alama". (Umaru)


1 2