Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-13 13:37:47    
Me ya sa Mr. Putin ya wargaza gwamnatin Rasha?

cri

A ran 12 ga wata, Mr. Putin, shugaban kasar Rasha ya karbi takarkar neman murbus da gwamnatin wadda firayim minista Mihail Fladkov ke shugabanta ta mika masa, kuma ya sa hannu kan umurnin shugaban kasa wanda ya yi shelar rusa gwamnatin kasar. A wannan rana da dare kuma ba zato ba tsammani Mr. Putin ya gabatar da sunan Victor Zubkov, shugaban hukumar sa ido kan harkokin kudi ta Tarayyar rasha da ya zama mai jiran zaben firayim ministan kasar. Ina dalilin da ya sa Mr. Putin ya wargaza gwamnatin Rasha? Kuma wane tasiri ne wannan aiki ya haifar ga ci gaban al'amuran siyasa na Rasha? Domin samun amsa wadannan tambayoyi, wakilanmu sun je neman labaru daga wajen Mr. Zhang Hong, mai yin bincike na hukumar binciken harkokin Rasha da na gabashin Turai da na tsakiyar Asiya ta cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin. To, ga cikakken bayanin.

Mutane sun sa lura cewa, wannan garambawul da aka yi a dandalin siyasa na Rasha an yi shi ne a lokacin da ya rage sauran watanni 3 kawai a gudanar da zaben Duma wato majalisar wakilan Rasha wanda za a yi a ran 2 ga watan Disamba. Mr. Zhang ya bayyana cewa, Mr. Putin yana da makasudin siyasa a bayyane wajen wargaza gwamnatin Fladkov a wannan lokaci. Ya ce, "Tun bayan da Mr. Fladkov ya ci zaben zama firayim minista zuwa yanzu, kullum ana yada jita-jita cewa zai yi murabus daga mukaminsa. Amma me ya sa shugaba Putin ya zabi wannan lokacin da ya canja gwamnatin Fladkov? Ina gani cewa, murabus da gwamnatin Fladkov ta yi ya zama share fage ne da shugaba Putin ya yi wajen siyasa domin babban zaben majalisar Rasha, kuma ya zama wani babban mataki ne da aka dauka tun kafin lokaci domin zaben shugaban kasar Rasha da za a yi a shekara mai zuwa."


1 2