Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-12 17:46:30    
Cin apple ga mata masu ciki zai iya taimaka wa yaransu wajen kare su daga cutar tarin asthma

cri

Ban da wannan kuma, a cikin wannan bincike, manazarta sun gano cewa, idan mata suna yawan cin kifi lokacin da suke da ciki, to yiyuwar kamuwa da cutar kyasfi ga yaransu zai samu raguwa sosai.

Haka ne, idan mata masu ciki sun kula da abincin da suka ci, to yaransu za su samu alheri sosai wajen lafiyar jiki.

Manazarta na kasar Japan sun gano cewa, idan mata masu ciki suka fara tauna cingam bayan da suka samu ciki har watanni shida, to, hadarin kamuwa da rubewar hakora ga jariranda suka haifa zai ragu da kashi 50 ckin dari.

Bida labarin da jaridar Tokyo News ta kasar Japan ta bayar a ran 13 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki, manazarta na jami'ar Okayama ta kasar sun gudanar da bincike ga mata fiye da 50, inda suka sa wadannan mata su tauna cingam uku a ko wace rana tun daga watanni shida bayan da suka samu ciki har zuwa watanni 9 bayan da suka haihu, ta yadda za a iya rage yawan munanan kwayoyi masu haddasa rubewar hakora da ke cikin bakunansu. Daga baya kuma manazarta sun gano cewa, game da jariran da shekarunsu ya kai 1 da rabi da haihuwa, hadarin kamuwa da rubewar hakora sakamakon gamuwa da irin wannan mumunar kwaya ga wadanda iyayensu mata su kan tauna cingam lokacin da suke da ciki ya ragu da kashi 50 cikin dari bisa na wadanda iyayensu mata ba su taba tauna cingam ba.

Manazarta suna ganin cewa, dalilin da ya sa jarirai su kan kamu da wannan mumunar kwaya shi ne sabo da iyaye mata su kan bai wa yaransu abinci bayan da suka tauna shi. Sabo da haka rage yawan munanan kwayoyi da ke cikin bakunan iyaye mata zai taka muhimmiyar rawa ga lafiyar bakunan jarirai, kuma tauna cingam wata dabara ce mai sauki wajen shawo kan cutar.(Kande)


1 2