Kamar yadda Sinawa su kan ce, idan ana cin apple guda a ko wace rana, to ba za a bukaci ganin likita ba. Yanzu wani sabon binciken da aka gudanar ya shaida wannan magana, wanda ya gano cewa, idan mata suna cia appale mai yawa lokacin da suke da ciki, to zai iya kare yaransu daga cutar tarin asthma a lokacin yarantakarsu.
Manazarta na kasar Holland da na sauran kasashe sun bayar da wani rahoto a kan mujallar Thorax ta kasar Amurka, cewa sun gudanar da wani bincike ga mata masu ciki kusan 2000 wajen abincin da su kan ci, daga baya kuma sun zabi yara 1253 da suka haifa domin ci gaba da gudanar da bincike gare su wajen wane irin tasiri ne al'adar cin abinci ga mata masu ciki zai bai wa yaransu a fannin hanyoyin numfashi.
Kuma manazarta sun bayyana cewa, binciken ya gano cewa, game da mata da su kan ci appale da yawa lokacin da suke da ciki, yiyuwar kamuwa da cutar tarin asthma ga yaransu ta yi kadan. Dalilin da ya sa haka shi ne watakila sabo da apple yana kunshe da wani sinadarin musamman, kamar sinadarin flavoid da dai sauransu.
1 2
|