Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-12 12:50:50    
Ya kamata kasashen duniya su hada kansu wajen yaki da ta'addanci daga dukkan fannoni

cri

Malam Li ya kara da cewa, a yayin da Amurka ta shirya kwarya-kwaryar bikin tunawa da hare-haren ta'addancin ran 11 ga watan Satumba, jagoran kungiyar al-Qaeda Osama Bin Laden ya bullo a daidai wannan lokaci a kan internet bayan da ya bace har dogon lokaci. Wannan ya nuna cewa, batun yaki da ta'addanci na da sarkakkiya sosai, haka kuma, Amurka ta ci tura ta fuskar yaki da ta'addanci a fannoni 2. Ya ce,'Da farko dai a harkokin yaki da 'yan ta'adda a duniya, Amurka ta rasa kyakkyawar dabara don murkushe tsarin kungiyar al-Qaeda da ke bazuwa a duniya. Na biyu kuma, bayan yakin kasar Afghanistan, musamman ma bayan yakin Iraq, matakan da Amurka ta dauka sun karfafa gwiwar karin 'yan ta'adda da su shiga tsarin kungiyar al-Qaeda, Amurka ta kauce wa babbar hanyar yaki da ta'addanci a yayin da take yaki da 'yan ta'adda a duniya, wannan ne dalili mafi muhimmanci da ya sa ba ta kama Bin Laden ba, ba ta kuma murkushe kungiyar al-Qaeda kwata kwata ba.'

Ta'addanci baranaza ce da kasashen duniya ke fuskanta. Malam Li ya yi hasashen cewa, kasashen duniya sun ci tura, sun kuma sami nasara a fannin yaki da ta'addanci, ya zuwa yanzu dai suna bukatar tinkarar matsaloli da yawa. Ya ce,'Tun bayan aukuwar hare-haren ta'addancin ran 11 ga watan Satumba, kasashen duniya sun sami dimbin sakamako wajen yin hadin gwiwa ta fuskar yaki da ta'addanci, sun bindiga da kuma kama jagora da kusoshi da yawa na kungiyar al-Qaeda, sa'an nan kuma, sun kara tono makarkashiyar ta'addanci da ke da nasaba da kungiyar al-Qaeda. Amma duk da haka kungiyar al-Qaeda na samun ci gaba, tana bazuwa a duniya, haka kuma, mun gano babbar matsalar da wannan kungiyar ke kawo wa kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci, wato 'yan kungiyar sun shiga muhimman hukumomin gwamnatocin kasashen duniya.'

Dadin dadawa kuma, malam Li ya nuna cewa, ba a sami tsarin yaki da ta'addanci da Majalisar Dinkin Duniya ke shugabanta ba tukuna. Ko da yake hadin gwiwar da ke tsakanin bangarori 2 a wasu yankuna na iya hana aukuwar hare-haren ta'addanci bisa wani matsayi, amma ba ta iya rage wuraren da 'yan ta'adda ke taruwa ba. Yana ganin cewa, yaki da ta'addanci na bukatar kasashen duniya su yi hadin gwiwa a tsakaninsu. Ba za a iya kawar da ta'addanci kwata-kwata ba, sai a yaki da shi bisa tsarin Majalisar Dinkin Duniya.(Tasallah)


1 2