Ran 11 ga wata rana ce ta cikon shekaru 6 da aukuwar hare-haren ta'addancin ranar 11 ga watan Satumba. Mutane da yawa sun gano cewa, in an kwatanta da kasaitattun bukukuwan tunawa da ta yi a da, a shekarar da muke ciki, kasar Amurka ta fara shirya bikin tunawa da wannan rana ba bisa babban mataki ba. Shin irin wannan canji ya nuna kananan sauye-sauyen da Amurka ke samu wajen yaki da ta'addanci? Malam Li Wei, darektan sashen nazarin yaki da ta'addanci ta cibiyar nazarin huldar da ke tsakanin kasashen duniya a zamanin yanzu ta kasar Sin ya yi bayani kan wasu batutuwan da ke shafar yaki da ta'addanci.
Malam Li na ganin cewa, a da don neman al'ummar Amurka da su goyi bayan aiwatar da manyan tsare-tsaren Amurka wajen yaki da 'yan ta'adda, ya zama wajibi a mayar da ran 11 ga watan Satumba a matsayin muhimmiyar ranar tunawa, an kuma yi gaggarumin bikin tunawa da wannan rana. Amma yanzu saboda sauye-sauyen halin da take ciki a gida da kuma waje, Amurka ta fito da sabon ra'ayi a fannin tunawa da hare-haren ta'addancin ran 11 ga watan Satumba. Malam Li ya ce,'Don me Amurka ta fara shirya bikin tunawar ba bisa babban mataki ba a wannan shekara? A ganina, daliai su ne. Da farko tun daga ran 11 ga watan Satumba na shekarar 2001 har zuwa yanzu, a galibi dai Amurka ta kafa cikakkun matakan yaki da ta'addanci a gida. Amma turan da ta ci ya fi nasarar da ta samu a fannin yaki da ta'addanci a duniya, shi ya sa Amurka ta shirya bikin ne domin tunanin matakan da ta dauka don yaki da ta'addanci a duniya.'
1 2
|