
Bayan wannan kuma, an canza hanyar ruwa ta tabkin Wulong, an hada ta da tabkin Daming a matsayin idon ruwa da mutane suka fito da shi. Ruwan da ke fitowa daga wannan idon ruwa yana kasancewa wata kyakkyawar karamar magangarar ruwa a yammacin gabar tabkin Daming. An dasa bishiyoyin willow masu yawa a gabobin tabkin, an kuma dasa dimbin furannin white lotus mai fadin murabba'in kadada 6.7 ko fiye a cikin tabkin. Ta haka, mutane suna iya ganin yadda magabatanmu suka gani a zamanin da, wato a gabobi 4 na wannan tabki, ana iya ganin furannin white lotus; a gabobi 3 na tabkin, an dasa bishiyoyin willow; birnin Jinan ya shahara ne saboda kyan ganin manyan duwatsu, kusan rabin wannan birni wani kyakkyawan tabki yana mamaye da shi. Wadannan rubutattun wakoki irin na kasar Sin malam Liu Fenggao ne ya rubuta a zamanin daular Qing na kasar Sin, ya sifanta kyan ganin birnin Jinan yadda ya kamata. A shekarar 1955, an maida takbin Daming ya zama wani wurin nishadi na tabkin Daming, inda al'ummar kasar ke kan ziyara.

Maziyarta su kan iya shiga wurin nishadin nan ta kofar kudu, kyakkyawan ginin da aka masa rumfa a sama wato 'Pailou' a bakin Sinawa, wanda aka yi masa jan kawa da kuma wasu babbakun zinariya na haruffan Sinanci da suka ratsa samansa, shi ne ake nufi da tabkin Daming, wato tabkin haske. Bayan ratsa kofa ta kudu, mutane suna juyawa hagu, sai masu yawon shakatawa su gane cewa, suna cikin layin inuwar bishiyoyin willow a gabobin tabkin.(Tasallah) 1 2
|