
Tabkin Daming mai fadin murabba'in kadada 46.5 ya kasance ne a arewacin tsohuwar unguwar birnin Jinan na lardin Shandong na kasar Sin, shi ne daya daga cikin manyan wuraren yawon shakatawa guda 3 a wannan birni.
Kafin shekara ta 1949, ruwa ya shanye a tabkin Daming. Tabo ya yi kusan mamaye wannan tabki. Amma duk da haka, bayan shekara ta 1949, sabuwar gwamnatin kasar Sin ta yashe tabo daga tabkin kwata-kwata. An yi kwaskwarima kan gabobin tabkin, an sake gina su da duwatsu. Sa'an nan kuma, an shimfida wata hanya da kwalta da duwatsu a kewayen wannan tabki. Ban da wannan kuma, an yi kwaskwarima ko kuma sake shafa fenti kan hasumiyoyi da rumfuna da hanyoyin da ke hada dakuna da manyan zaure da gidajen ibada, wadanda suke kasancewa a gabobin tabkin, ko kuma suke kewayen manyan duwatsu. Dadin dadawa kuma, an gina wani filin wasan yara, da kuma filin wasan roller-skating da kuma wani lambun furanni a dab da tabkin Daming. An kuma fito da na'urori don ba da hidimomi ga masu yawon shakatawa da ke sha'awar tukin kwale-kwale.
1 2
|