Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 15:57:59    
An bude taron shekara-shekara na farko na Davos na yanayin zafi a Dalian na kasar Sin

cri

Daga baya, Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, kasar Sin za ta gaggauta sauya salon da take bi wajen bunkasa tattalin arziki ,da kara karfin da take da shi na yin kirkire-kirkire tare da cin gashin kai, da kuma kara kyautata harkokin kiyaye ikon mallakar ilimi da kuma daga matsayin kimiyya da na fasaha na masana'antun kasar daga dukkan fannoni. A lokaci daya, za ta kara sa ido kan ingancin kayayyaki.

Bugu da kari kuma, Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar damanufar bude kofa ga kasashen waje, da kara yin hadin gwiwa tare da sauran masana'antu da kamfanoni na kasashe daban-daban na duniya bisa jigon zaman daidai wa daida da samun moriya da juna. Ya furta cewa : " Sabbin jagoran bunkasa tattalin arziki sun kasance tamkar wani irin sabon karfi ne na aka samu lokacin da ake sauya tsarin tattalin arzikin duniya, musamman ma kamfanoni da masana'antu masu tasowa na duniya sun fi samun rayayyen karfi da kuma karfin yin takara da na bunkasuwa, wadanda kuma suke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin da ake yi a duk duniya."

A karshe dai, shugaban dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na yanzu Mr. Klaus Schwab ya yi jawabin fatan alheri a gun bikin, inda ya furta cewa: " Shin ko sabbin jagoran bunkasa tattalin arziki na karon farko za su iya tabbatar da samun nasara. Game da wannan dai, ina da ra'ayoyi guda uku, wato na farko a kalla a kulla wata sabuwar huldar abokantaka ta hadin kai a duk duniya don kara daukaka ci gaban harkokin da abin ya shafa; na biyu, a kalla a tsara wani shiri dake da idon basira na muhimman tsare-tsare don janyo kyakkyawan tasiri ga bunkasuwar masana'antu da kamfanoni; Ra'ayina na uku wata na karshe da ya fi muhimmanci shi ne a mai da mu don mu zama masu rikon amana da matuka na gaskiya wadanda za su tsara makomarsu ta kansu". ( Sani Wang)


1 2