Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 15:57:59    
An bude taron shekara-shekara na farko na Davos na yanayin zafi a Dalian na kasar Sin

cri

An gudanar bikin bude taron shekara-shekara na farko na Davos na yanayin zafi a ranar jiya da maraice a birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. Wannan ne karo na farko da hukumar dandalin tatttaunawa kan tattalin arzikin duniya ta gudanar da taron shekara-shekara na duk duniya a nan kasar Sin. Firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya halarci bikin bude taron, inda ya yi jawabin cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen bin hanyar samun dauwamamen ci gaba; Sa'annan za ta sanya matukar kokari wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da sauri kuma cikin dogon lokaci; kuma tana so ta kara yin hadin gwiwa tare da kasashe daban-daban da kuma kamfanoni da masana'antu don daukaka ci-gaban yunkurin bunkasa tattalin arzikin duk duniya kamar yadda ya kamata.

Ana mayar da "Dandalin tattaunawa kan tattallin arzikin duniya" a matsayi wani dandalin tattaunawa na matakin koli na kasa da kasa da ba na gwamnati ba, wanda yanzu yake da mambobi sama da dubu daya, wadanda dukanninsu shahararrun masana'antu da kamfanoni ne na wurare daban-daban na duniya.

A gun bikin bude taron, Mr. Wen Jiabao ya bayyana wa wakilai mahalartan taron yanayin da ake ciki yanzu a fannin bunkasa tattalin arziki da kuma matsalolin da ke gabanta game da wannan fanni. Ya furta cewa, a takaice dai yanayin yanzu na bunkasuwar tattalin arzikiin kasar Sin yana da kyau, amma kuwa ya kasance da wasu matsaloli dake gabanta kamar na an samu karuwar kadarori cikin sauri fiye da kima, kuma yawan rancen kudi da samar ya yi yawa; kazalika, yawan rarar kudin da aka samu daga cinikin waje ya yi yawan gaske; dadin dadawa, kasar Sin ta samu babban matsi daga hauhawar farashin kaya. Mr. Wen Jiabao ya fadi cewa: " A halin yanzu dai, wajibi ne a mayar da aikin jan birki ga bunkasa tattalin arzikin kasar cikin sauri fiye da kima a matsayin daya daga cikin ayyukan daidaita harkokin tattalin arzikin kasar daga dukkan fannoni; Sa'annan a ci gaba da ingiza gyare-gyaren tsarin musayar kudi".

1 2