Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-05 17:03:06    
Shakar hayakin taba zai yi illa ga lafiyar baka

cri

Sakamakon gwajin ya nuna cewa, muddin berayen sun yi zama a cikin muhallin da ke da hayakin taba, ko kuma sun shaki hayakin taba kadan ko da yawa, sun fi saukin samun lalacewar sinadari kamar kashi da ke kan hakoransu idan an kwatanta su da wadanda suka yi zama a cikin muhallin da babu hayakin. Kuma manazarta sun yi bayanin cewa, lalacewar sinadarin kashi shi sanadi ne mafi muhimmanci da ke haddasa zubewar hakora ga mutanen da suke fama da cutar hakora.

Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, kafin wannan, an riga an shaida cewa, ana kasance da dangantakar da ke tsakanin shan taba da cutar hakora, amma gwajin da suka yi ya bayyana cewa, shakar hayakin taba shi ma yana iya yin illa ga lafiyar baki.

Preston Miller, shugaban kungiyar kula da cutar hakora ta kasar Amurka ya bayyana cewa, ta wannan gwaji, mutane sun iya fahimtar cewa, shakar hayakin taba yana da illa sosai. Idan ana son kiyaye hanyar zaman rayuwa lami lafiya kamar yadda ya kamata, dole ne a bar wuraren da ke cike da hayakin taba da yawa. Bugu da kari kuma Mr. Miller ya ce, an riga an fara aiwatar da umurnin hana shan taba a wuraren jama'a kamar dakunan cin abinci da dai sauransu a wasu biranen kasar Amurka, kuma kungiyar kula da cutar hakora ta Amurka ta nuna amincewa sosai kan wannan batu. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba kawai mutane suna iya cin abinci cikin farin ciki ba, har ma za a ba da taimako wajen kiyaye lafiyar bakunansu.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani daban kan shawo kan cututtuka. A wasu wuraren da ke da wuyar zuwa na kasar Sin, wasu cututtuka masu tsanani suna kawo wa lafiyar mazauna barazana sosai. Sabo da haka gwamnatin lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin ta gabatar da wani muhimmin mataki wajen shawo kan cututtuka masu tsanani. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku kan wannan batu.


1 2