Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shakar hayakin taba zai yi illa ga lafiyar baka, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan matakan musamman da lardin Qinghai na kasar Sin ke dauka domin shawo kan cututtuka masu tsanani.
Manazarta na kasar Amurka sun buga wani rahoto kan mujallar ilmin cutar hakora a watan Afril na shekarar da muke ciki, cewa sakamakon gwajin dabbobi ya bayyana cewa, shakar hayakin taba yana iya yin illa ga lafiyar baki, wato mai yiyuwa ne zai haddasa lalacewar wani sinadari kamar kashi da ke kan hakora game da mutanen da suke fama da cutar hakora.
A cikin gwajin da manazarta suka yi, da farko sun sa beraye sun kamu da cutar hakora. Daga baya kuma sun kasa wadannan beraya cikin rukunoni uku. Beraye na rukuni na farko suna zama a cikin muhallin da babu hayakin taba, na rukuni na biyu kuma suna zama a cikin muhallin da ke da hayakin taba kadan har kwanaki 30, yayin da na rukuni na uku suke zama a cikin muhallin da ke cike da hayakin taba har kwanaki 30.
1 2
|