Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 17:55:09    
Kallon gauraki masu jan wuya a shiyyar kare halitta ta Zhalong

cri

Ruwa na da matukar tsabta a shiyyar kare halittu ta Zhalong. Gauraki masu jan wuya suna ciyar da kansu da kifaye da jatan lande da bawon kifi da saiwoyin tsire-tsire. Da kyar mutane ke iya shiga shiyyar kiyaye halittu ta Zhalong saboda ciyayi masu tsawon mita 1 zuwa mita 3 a wajen, shi ya sa wadannan tsuntsayen ruwa masu daraja suka sami kyakkyawan sharadi wajen rayuwa da hayayyafa. A watan Maris na ko wace shekara, lokacin bazara ya yi, gauraki masu jan wuya masu yawa sun zo nan domin kafa shekansu da yin rayuwa da kuma jefa kwai da yin hayayyafa daga wurare masu nisa a kudancin kasar Sin.

Don kiyaye muhalin halittu a wajen, hukumar wurin ta kebe wani wuri da ke dab da danshin wuri a matsayin wurin nishadi, ta hana masu yawon shakatawa su shiga danshin wuri. Mutane na iya hango wuri mai danshi da kuma gauraki masu jan wuya a cikin hasumiyar Wanghe mai tsayin mita 30.

Sa'an nan kuma, don kiyaye irin wadannan tsuntsaye masu daraja, shiyyar kare halitta ta Zhalong ba kawai ta kiyaye wadanda ke rayuwa a daji yadda ya kamata ba, har ma ta hayayyafar wadannan tsutsanye ta hanyar zamani. Wannan shiyya ta riga ta ksance sansanin hayayyafar tsuntsun red-crowned crane ta hanyar zamani mafi girma a kasar Sin. Malam Wang Kun ya yi bayani cewa, ana hayayyafar irin wannan tsuntsu ta hanyar zamani ne bisa al'adar rayuwa, wadanda ke rayuwa a daji. Ya ce,

'Iyayen kananan gauraki masu jan wuya iyaye su kan haifar da kwayaye 2 kawai a ko wace shekara. A karshen watan Oktoba zuwa farkon watan Nuwamba na ko wace shekara, su kan zo kudancin kasar tare da 'ya'yansu. A lokacin baraza na shekara ta gaba, su kan dawo tare da su, su kan taimake su don su yi rayuwa da kansu. Daga baya kuma, iyayen su kan sake yin kiwon sabon rai. Ma'aikatanmu mu kan debo daya daga kwayayensu 2 daga shekansu don yin hayayyafar tsuntsayen ta hanyar zamani. Iyayen su kan sake jefa guda daya a cikin shekansu. In ka debo dukkan kwayaye 2, su kan sake jefa wasu 2, in ka debo wadannan kwayaye 2, to, iyayen sun bar wannan wuri, ba su dawo ba, saboda ba su iya hayayyafar 'ya'yansu bisa kyakkyawan yanayin kwanciyar hankali a wajen ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ana kira tsuntsun red-crowned crane alama ce ta nuna ingancin muhalli. Wurin da wannan irin tsuntsu ke rayuwa, wuri ne inda yake kasancewa da muhalli mafi kyau.'

Don biyan bukatun masu yawon shakatawa na kusantad da gauraki masu jan wuya, ma'aikatan wurin sun ware wata fadama a shiyyar, inda aka saki gauraki masu jan wuya da mutane ke kiwo a daidai lokacin da aka tsara, wadannan tsuntsaye su iya tashi cikin 'yanci. Malam Xu Jianfeng, mai aikin kiwon gauraki masu jan wuya, ya ce, gauraki masu jan wuya da mutane ke kiwo suna da ban sha'awa, ba su ji tsoron mutane ba, sun kulla kyakkyawar hulda a tsakaninsu da masu aikin kiwonsu.

Malam Xu ya kara da cewa, masu aikin kiwon gauraki masu jan wuya su kan dudduba wadannan tsautsaye sau 3 a ko wace rana, sun gano cewa, ko hankulansu sun canja ko a'a. In su kamu da ciwo, su kan nuna halin bacin rai kamar yadda mutane suke yi. In suna koshin lafiya, to, gauraki masu jan wuya da ke iya fahimtar mutane sosai su kan yi kuka cikin farin ciki a yayin da masu aikin kiwonsu suka matsa musu, sa'an nan kuma, su ka yi rawar jiki.

A ko wace shekara, shiyyar kare halittu ta Zhalong ta kan karbi masu yawon shakatawa masu dimbin yawa da ke neman more idanunsu da wadannan kyawawan tsuntsaye. Masu yawon shakatawa sun nuna babban yabo kan kyan karkara da suke gani, wato dan Adam da muhalli suna zaman tare cikin jituwa. In kuna da sha'awa, to, ya fi kyau ku zo shiyyar kare halitta ta Zhalong da kanku, ku kalli gauraki masu jan wuya da kanku.

 

 


1 2