Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 17:55:09    
Kallon gauraki masu jan wuya a shiyyar kare halitta ta Zhalong

cri

A lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, akwai wata shiyyar kiyaye halittu mai suna Zhalong, wadda ta shahara a gida da kuma a ketare. Ciyayi na girma sosai a cikin ruwa, sa'an nan kuma, ana iya ganin dimbin tsire-tsire da tabkuna da fadamomi masu fadi a wajen. Ita ce aljannar tsuntsaye, haka kuma, tana daya daga cikin muhimman wuraren da gauraki masu jan wuya ke rayuwa, shi ya sa ana kiransa garin gauraki masu jan wuya.

Shiyyar kare halittu ta Zhalong ta kasance daya daga cikin muhimman wurare masu danshi a duniya, fadinta ya kai misailn kadada dubu 210. A wannan shiyyar, ciyayi masu tsawo suna girma sosai a cikin fadamomi masu fadi, ana kuma samun kifaye da jatan lande masu yawa, ita ce aljannar tsuntsaye wajen yin hayayyafa. Malam Wang Kun, wani ma'aikacin da ke aiki a shiyyar kare halitta ta Zhalong, ya yi karin bayanin cewa, 'Don me shiyyar kare halitta ta Zhalong ta shahara a duk duniya? Dalilai su ne da farko, ita ce danshin wuri mafi girma a kasar Sin, har ma a duk Asiya, inda aka samu dimbin ciyayi masu tsawo a fadamomi masu fadi, ta kuma zama ta hudu a tsakanin dukkan danshin wurare a duniya saboda girmanta. Na biyu kuma, shiyyar na da dogon tarihi, sa'an nan kuma, mutane na ta kyautata akidar kiyaye danshin wurare, shi ya sa ba su kai mata babbar barna ba.'

A matsayin daya daga cikin muhimman wuraren da gauraki masu jan wuya ke rayuwa, ana samu gauraki masu jan wuya mafiya yawa a shiyyar kare halitta ta Zhalong. Madam Liu Na, mai jagorancin masu yawon shakatawa ta ce, sunan tsuntsun red-crowned crane daban shi ne Xianhe, akwai wata almara game da shi a wurin. Tana ganin cewa, ba a iya raba danshin wuri na Zhalong da tsuntsun Xianhe ba. Ta ce, 'Dodanni 2 wato dragons a Turance mai launin baki da mai launin fari da suka zo daga kogin Heilongjiang sun ta da rikici, sun yi kwanaki 49 suna ta yaki da juna, a karshe dai bakin dragon ya lashe farin dragon, amma ya ji mummunan rauni, har ma bai iya komawa kogin Heilongjiang ba, ya fado zuwa doron kasa, ya haifar da wani babban rami a kasa. Tsuntsayen Xianhe sun nemi kubutad da shi, sun diba ruwa daga wuri mai danshi, sun zuba ruwan cikin ramin don taimake shi. Sannu a hankali, takunan da muka gani a yau sun bullo.'

1 2