Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 17:36:54    
Gidan ibada na Daming a birnin Yangzhou na lardin Jiangsu

cri

 A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan gidan ibada na Daming da ke birnin Yangzhou na lardin Jiangsu, daga bisani kuma, za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, babban tsaunin Aershan, muhimmin bangare ne na manyan tsaunukan Daxing'anling.

Gidan ibada na addinin Buddha na Daming yana cikin birnin Yangzhou na lardin Jiangsu na kasar Sin, wanda wani bangare ne na gine-ginen da ke da bangarori da yawa. An fara gina shi a karni na 5.

Gidan ibada na Daming ya kulla hulda mai inganci a tsakaninsa da kasar Japan. An ce, an gayyaci dan addinin Buddha mai suna Jian Zhen, wanda aka haife shi a shekarar 688 bayan haihuwa Annabi Isa, A.S., ya kuma rasu a shekarar 763 bayan haihuwa Annabi Isa, A.S., da ya ba da ilmin addinin Buddha a kasar Japan. Sau biyar Jian Zhen ya yi yunkurin zuwa kasar Japan, amma ya sha kaye. A karo na shida ne Jian Zhen yake yunkurin zuwa kasar Japan, ko da yake a lokacin can, shekarunsa ya kai 66 da haihuwa, kuma ya kasance makaho, bai iya ganin kome ba. Amma duk da haka, ya ci nasara a karshe, ya isa birnin Nara, hedkwatar kasar Japan a can can can da, ya kafa wata cibiyar koyarwa a wani gidan ibada na addinin Buddha a wurin. A shekarar 1963 da ta gabata, wato shekara ce cikon shekaru 1200 da rasuwar wannan mashahurin dan addinin Buddha, dimbin 'yan addinin Buddha na kasashen Sin da Japan sun gina wani babban zauren tunawa da marigayi Jian Zhen don tunawa da gudummowar da Jian Zhen ya bayar wajen kara fahimtar Japanawa kan kasar Sin a fannonin adabi da fasaha da ilmin tsarin gine-gine da ilmin likitanci da dab'i. A kan ganuwar wannan babban zaure, an yi zane-zane game da tafiye-tafiyen da Jian Zhen ya yi. A shekarar 1980 da ta wuce, 'yan addinin Buddha na kasar Japan sun ba da wani mutum-mutumin katako na Jian Zhen a matsayin abin kyauta, wanda wani kwafi ne na kyakkyawan mutum-mutumin wannan dan addinin Buddha da aka shafa masa fenti, an kuma ajiye shi a gidan ibada na Nara a kasar Japan.

1 2