Na biyu, a yi aikin share fage ga jibge rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na hadin guiwar majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar Afrika wadanda yawan sojojinsu zai wuce 26,000. Aikin jibge sojojin nan a yankin Darfur, aiki mai nauyi ne da majalisar dinkin duniya za ta yi don jigbe sojoji mafiya yawa a yanki mai sarkakiyyar gaske. Sabo da lalacewar muhalli da karancin ruwa da sauransu, shi ya sa ko ta yaya ba za a sami nasara wajen yin wannan aiki ba sai an sami hadin kai daga wajen gwamnatin kasar Sudan. Da ganin haka, a lokacin ziyararsa, Mr Ban Ki-moon zai bukaci gwamnatin Sudan ta yi namijin kokari wajen ba da taimako ga jibge sojojin kiyaye zaman lafiya tun da wuri, kuma ta nuna goyon baya yadda ya kamata.
Na uku, a nemi samun taimako da goyon baya daga bangarori daban daban don aiwatar da shirin ba da ajin jin kai ga 'yan gudun hijira na kasar Sudan sama da miliyan 2, da kuma komar da su gida. Mr Ban Kim-moon zai yi ziyara a kasar Chadi wadda ta karbi 'yan gudun hijira na Darfur da yawansu ya wuce dubu 200, makasudinsa shi ne domin neman kasar Chadi da ta amince da majalisar dinkin duniya ta jibge sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar yadda ya kamata don kare 'yan gudun hijira.
Manazarta sun nuna cewa, jibge sojojin kiyaye zaman lafiya da daidaita batun 'yan gudun hijira wani aiki ne da za a yi don neman daidaita batun Darfur. Asali ma dai gaggauta bunkasa harkokin siyasa a Darfur shi ne babban aiki da za a yi don tabbatar da zama lafiya mai dorewa a yankin. A halin yanzu, manya da kananan kungiyoyi masu adawa da gwamnati sun wuce goma a Darfur. Suna nuna ra'ayoyinsu daban daban a kan batun rarraba ikoki da dukiyoyi, kuma suna ta jawo wa kansu baraka. Duk wadannan wahala ce da ake sha wajen daukar matakan tsaro da daidaita batutuwan filaye da na jin kai da sauransu. Wannan dalilin ne da ya sa, Mr Ban Ki-moon ya ga tilas ne ya yi taka tsantsa wajen yin harkoki a kan batun Darfur. 1 2
|