Ran 3 ga wata, Mr Ban Ki-moon, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya fara yin ziyarar aiki ta kwanaki 6 a kasar Sudan da kuma Chadi da Libya wadanda ke makwabtaka da ita.
Tun bayan da ya zama babban sakataren a watan Janairu da ya wuce, kullum Mr Ban Ki-moon yana dora muhimmanci sosai ga batun Darfur, yana fatan zai ba da taimako wajen daidaita wannan batu. A gun taron kasa da kasa kan batun Darfur da aka shirya a garin Arusha na kasar Tanzaniya a farkon watan Augusta da ya wuce, wasu kungiyoyin dakaru masu adawa da gwamnati na Darfur wadanda suka halarci taron, sun amince da yin shawarwarin karshe a tsakaninsu da gwamnatin Sudan bisa matsayi daya a cikin watanni uku masu zuwa, wannan ya zama sabuwar alama ga daidaita batun Darfur cikin lumana. A cikin irin wannan hali ne, Mr Ban Ki-moon yake fatan ziyararsa za ta inganta sakamako mai yawa da aka samu a kan batun Darfur, ta samar da sharuda ga daidaita wannan batu. Manyan batutuwa uku da suke shafar ziyarar da Mr Ban Ki-moon ke yi a kasashen Afrika uku su ne, sa kaimi ga bangarori daban daban da su bunkasa harkokin siyasa da girke sojojin kiyaye zaman lafiya da kuma batun 'yan gudun hijira.
Na daya, a bunkasa harkokin siyasa a Darfur don sa kaimi ga bangarori daban daban da su shiga shawarwarin sulhu na karshe tun da wuri. Sabo da haka a lokacin ziyararsa a kasar Sudan, Mr Ban Ki-moon zai sa kafa a yankin Darfur don kai ziyara ga wasu wuraren 'yan gudun hijira na yankin, kuma zai yi shawarwari a tsakaninsa da Mr Omar al-Bashir, shugaban kasar Sudan. Haka kuma zai gana da wasu shugabannin yankin Darfur, inda zai bukace su da su nuna biyayya ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka daddale. Ka zalika a lokacin ziyararsa a kasar Libya, Mr Ban Ki-moon zai bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da taka rawa sosai wajen sa kaimi ga kungiyoyin dakaru daban daban na Darfur da su koma kan teburin shawariwari.
1 2
|