Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-03 21:38:20    
Ana bunkasa harkokin dab'i ta hanyar zamani cikin sauri a kasar Sin

cri

A halin yanzu, yawan ire-iren littattafai a kan Internet da kasar Sin ta gabatar ya kai kusan dubu 300, wato ke nan ya kai matsayin farko a duk duniya. Littattafan sun shafi al'adun dan adam da tattalin arziki da kimiyya da sauran fannoni daban daban. Ko da yake kasar Sin ta bunkasa harkokin dab'I ta hanyar digital cikin sauri sosai, amma duk da haka ya kasance da gibi da ke tsakaninta da kasashe masu sukuni. A kwanakin baya ba da dadewa ba, an taba shirya taron koli a kan harkokin dab'i ta hanyar digital a birnin Beijing.

Yayin da Malam Sun Shoushang, mataimakin shugaban babbar hukumar kula da harkokin watsa labaru da dab'i ta kasar Sin ke halartar wannan taron, ya bayyana cewa, yanzu, kasar Sin ta riga ta tsara babbar manufar bunkasa harkokin dab'i ta hanyar digital. Ya ce, "nan gaba, kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen gudanar da harkokin dab'i ta hanyar digital. Za ta gaggauta bincike da tsara manyan ma'aunan sana'ar dab'i da na fasaha mai muhimmanci, ta kokarta sosai wajen binciken fasaha ta yadda za a sami babban ci gaba a fannonin fasahar kiyaye ikon mallakar ilmin dab'i ta hanyar digital da sauransu."

Yanzu, yawan mutanen kasar Sin da ke amfani da tashar Internet ya riga ya wuce miliyan 100, ya kai matsayi na biyu a duniya. Don haka mutanen Sin sun fara canja hanyoyi da suke bi wajen yin karatu, mutane da ke karanta littattafai da ke kan Internet kullum sai kara karuwa suke yi. Sabo da haka ana da kyakkyawar makomar bunkasa harkokin dib'i ta hanyar digital. Malam Sun Shoushang ya nuna cikakken imaninsa ga makomar bunkasa harkokin dab'i ta hanyar digital a kasar Sin. Ya ci gaba da cewa,

"bisa babban goyon baya da gwamnatin kasar Sin ke nunawa, da kuma babban kokari da 'yan kasuwa masu samar da fasahar digital da hukumomin dab'i ke yi, tabbas ne, za a bunkasa harkokin dab'i ta hanyar digital da kyau kuma cikin sauri a kasar Sin, sa'an nan za a shiga wani sabon lokaci na kara bunkasa harkokin watsa labaru da na dab'i a kasar Sin."

Malam Sun Shoushang ya gabatar da shawara cewa, ya kamata, 'yan kasuwa masu binciken fasahar dab'i ta hanyar digital da 'yan kasuwa masu samar da kayayyakin digital da 'yan kasuwa masu sayar da kayayyakin digital su kara yin ma'amalarsu, su kara kwarewa wajen kula da abubuwan dab'i ta hanyar digital, su kara samun ribar kudi daga hidimarsu, ta yadda kasar Sin za ta kara daga matsayin fasahar dab'i ta hanyar digit da kara samun karfin takara a duniya. (Halilu)


1 2